Matatar mai ta Omega Butler matatar mai ce da ake shirin ginawa a kan fili mai girman eka 121 a jihar Rivers, Najeriya. Za ta sami karfin ganga 20,000 a kowace rana, tare da samar da kashi 90% na kayayyakin mai haske (Light Oil products). Da zarar an kafa matatar, za ta rage kudin man fetur, da samar da ayyukan yi har guda 1500, da kuma taimakawa wajen bunkasar tattalin arzikin jihar.

Matatar mai ta Omega Butler
Wuri

Tun daga lokacin an ba da lasisin aiki daga Sashen Albarkatun Man Fetur (DPR) don sauƙaƙe farawa da aiwatar da aikin.[1] A ranar 27 ga watan Mayu, 2015, an bayyana cewa an ware Naira biliyan 96 (dalar Amurka miliyan 480) don sayan aikin injiniyan, gine-gine, kulawa da ayyukan gudanar da ayyuka.[2]

Duba kuma gyara sashe


Manazarta gyara sashe

  1. "Rivers State Government Gets License For Omega Butler Refinery" . Government of Rivers State . 5 August 2013. Retrieved 28 May 2015.
  2. Duke, Russel (27 May 2015). "New Refinery Plus 1,500 New Jobs Coming to Rivers State and Nigeria" . The Guardian . Retrieved 28 May 2015.