Masallacin Abdülhamid II
Masallacin Abdülhamid II
Masallacin Abdülhamid II | |
---|---|
Wuri | |
Coordinates | 11°35′36″N 43°08′31″E / 11.5933°N 43.1419°E |
History and use | |
Opening | 29 Nuwamba, 2019 |
Maximum capacity (en) | 6,000 |
Karatun Gine-gine | |
Style (en) | Ottoman architecture (en) |
Yawan fili | 13,000 m² |
|
masallaci ne a cikin Garin Jibuti.[1] Shine masallaci mafi girma a Djibouti.
An kammala shi a cikin shekarar 2019, Gidauniyar Diyanet ta Turkiyya ce ta dauki nauyinta. An sanya masa suna ne bayan Sarkin Ottoman Abdulhamid II. Ginin, wanda aka gina shi da salon Usmaniyya, yana da damar daukar mutane 6,000.
Tarihi
gyara sasheAn tattauna batun tunanin masallacin ne a shekarar 2015, a ganawar da shugaban Djibouti, Ismail Omarelle da shugaban Turkiyya Erdogan.[2] An gina masallacin ne a kan wasu filaye da aka kwato. An bude masallacin ne a shekarar 2019. An bude masallacin ne tare da Firaminista Abdoulkader Kamil Mohamed.[1]
Gine-gine
gyara sasheMasallacin an gina shi ne da salon farfado da Daular Usmaniyya.[3] Yana da minarets guda biyu masu tsayin mita 46, da kuma kwazazzabo na tsakiya.
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Djibouti's biggest mosque, a gift from Turkey, opens". en.hawzahnews.com (in Turanci). 2019-11-30. Retrieved 2021-01-30.
- ↑ Welle (www.dw.com), Deutsche. "Mosques in Africa: A test of strength in the Middle East | DW | 18.12.2019". DW.COM (in Turanci). Retrieved 2021-01-30.
- ↑ Services, Compiled from Wire (2019-11-25). "Djibouti's biggest mosque, courtesy of Turkey, counts down to opening". Daily Sabah (in Turanci). Retrieved 2021-01-30.