Masa,uda Ibrahim
Masa'uda Ibrahim Yar Agadaz jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa wato kanniwud, sannan Kuma furodusa ce masana'antar fim tayi fina finai da dama a masana'antar yanzun take tashen ta. Ta fito a Shirin fim Mai dogon zango na Tashar Arewa 24 Mai suna DADIN KOWA inda ta fito a suna zuby , [1]shine fim din da ya daukaka ta a idon duniya kowa ya San ta.[2]
Takaitaccen Tarihin Ta
gyara sasheMasa'uda Ibrahim an haife ta a ranar 13 ga watan [3]nuwamba a garin agadaz. Haifaffiyar kasar nijar ce ta girma acan tayi karatun firamare da sakandiri a garin agadaz. Bayan ta gama ta zo jihar Kano ta shiga masana'antar fim ta Hausa wato kanniwud, an Fi sanin ta da yar agadez a masana'antar. Fim din da ya Kara fito da ita shine fim din"yar agadez " Wanda darakta aminu Saira ya Bada umarni , Umar S k mazugal yayi furodusin da Kuma nura Umar UK Wanda su kayi a shekarar 2011, tare da jarumi sani danja, Ibrahim maishinku,da Kuma nafisa Abdullahi, Zainab indomie, shine fim dinta na biyu a masana'antar. Tana kwaikwayon salon Tsohuwar jaruma safiya Musa, wacce suka zo suka zama kawaye. Ta shigo masana'antar fim a shekarar 2010 ta hannun furodusa Umar S K mazugal. Itace C.E.O na kamfanin Yar Agadez investment .[4]
Fina finan ta
gyara sashe- Yar Mai ganye
- Daga aure na
- Yar agadez
- gidan mijinah
- Wata mata ce
- Gida uku
- Rayuwa sirri ce
- Ishara
- inda Rai
- Sama da Fadi
- mugun zama
- Mijin Fatima
- mai laya
- Daga aure na
- Madafar kaunah
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://m.youtube.com/channel/UCT6mpU6GVo38dylNmIC8-1A
- ↑ https://www.hausaloaded.com/2019/11/hrkar-fim-na-kunshe-da-mahassada-cikin.html
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-31. Retrieved 2023-07-31.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-31. Retrieved 2023-07-31.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-31. Retrieved 2023-07-31.