Maryam Endowment Fund Ta kasance Ƙungiya ce ta jin-kai mai zaman kanta wacce take taimakon gajiyayyu a Faɗin Jihar Katsina da Faɗin Najeriya. Alh. Sani Zangon-Daura shine wanda ya assasata a shekarar 1982. Ayyukanta sun haɗa da samar da tallafin karatu ga iyalai masu ƙaramin karfi kama daga Firamare, makarantar gaba da Firamare, da kuma makarantar gaba da Sakandare, Kiwon Lafiya, Ciyarwa, tufatar wa, samar da likafani, gina masallatai da islamiyyu da sauran ayyuka na jin ki.