Mário Jorge Pasquinha Évora (an haife shi a ranar 28 ga watan Janairu 1999) ƙwararren ɗan ƙwallon ƙafa ne na Cape Verde wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron gida ga kungiyar ƙwallon ƙafa ta São João de Ver da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Cape Verde.

Mario Évora
Rayuwa
Haihuwa 28 ga Janairu, 1999 (25 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 

Aikin kulob gyara sashe

Évora samfurin matasa ne na Porto, kuma ya fara babban aikinsa a ƙungiyar Águeda a cikin shekarar 2018 a Campeonato de Portugal.[1] Ya koma Vitória B a ranar 2 ga watan Agusta 2020.[2] A ranar 30 ga watan Yuni 2022, kwangilarsa ta ƙare tare da Vitória B. [3] Jim kaɗan bayan ya koma São João de Ver a kakar 2022-23. [4]

Ayyukan kasa da kasa gyara sashe

An fara kiran Évora zuwa tawagar kasar Cape Verde a watan Oktoba 2017. [5] Ya buga wasansa na farko na ƙwararru tare da Cape Verde a wasan sada zumunci da suka yi rashin nasara da ci 2–1 a hannun Guinea a ranar 10 ga watan Oktoba 2020.[6]

Manazarta gyara sashe

  1. "Guarda-redes Mário Évora é reforço do Vitória de Guimarães | DTudo1Pouco" . dtudo1pouco.com .
  2. "Vitória apresenta guarda-redes com passado na formação do FC Porto" . www.ojogo.pt .
  3. "V. Guimarães arruma a casa e anuncia rescisão de contrato com sete jogadores" . www.ojogo.pt .
  4. "Igualdade entre Fafe e São João de Ver" . FPF .
  5. "Mário Évora estreia na convocatória dos Tubarões Azuis" .
  6. Strack-Zimmermann, Benjamin. "Cape Verde vs. Guinea" . www.national-football-teams.com .

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe