Marie Lebihan
Marie Lebihan yar siyasan Nijar ce. Tana daga cikin rukunin mata na farko da aka zaɓa a Majalisar Dokoki ta ƙasa a shekarar 1989.
Marie Lebihan | |||
---|---|---|---|
1989 - 1991 | |||
Rayuwa | |||
ƙasa | Nijar | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | National Movement for the Development of Society (en) |
Tarihin rayuwa
gyara sasheMemba na National Movement for the Development of Society (MNSD), Lebihan an tsayar da shi a matsayin dan takarar Majalisar Tarayya a Maradi a zaɓen shekarata 1989 . Kasancewar MNSD ita ce jam’iyya ɗaya tilo ta doka, an zabe ta ba tare da hamayya ba, ta zama daya daga cikin rukunin farko na mata biyar da aka zaɓa a Majalisar Dokoki ta Kasa. [1] An rusa majalisar ƙasa a shekarata 1991 kuma ba a sake zabenta a zaɓen shekarar 1993 ba .
Manazarta
gyara sashe- ↑ Alice J. Kang (2015) Bargaining for Women's Rights: Activism in an Aspiring Muslim Democracy, pp117–118