Marie-Rose Nizigiyimana
Marie-Rose Nizigiyimana (an haife ta a shekara ta 1966) 'yar siyasar Burundi ce. Ta riƙe muƙamin ministar kasuwanci, masana'antu, gidan waya da yawon buɗe ido a gwamnatin shugaba Pierre Nkurunziza daga ranar 18 ga watan Fabrairun 2014 har zuwa lokacin da aka kore ta a ranar 18 ga watan Mayun 2015.
Tarihin Rayuwa gyara sashe
An haifi Nizigiyimana a shekarar 1966 a unguwar Rango a lardin Kayanza.[1] Ta sami digiri a fannin tarihi a Jami'ar Burundi, kuma ta yi aiki a matsayin malama tun a shekarar 1993.[1]
Nizigiyimana ta kasance memba na jam'iyyar siyasa Union for National Progress tun a shekarar 1993.A ranar 18 ga watan Fabrairu 2014, an naɗa ta ministar kasuwanci, masana'antu, gidan waya da yawon buɗe ido bayan da aka yi wa majalisar ministoci garambawul.[2]
An kore ta ne a ranar 18 ga watan Mayu 2015, jim kaɗan bayan juyin mulkin da bai yi nasara ba.[3] Nizigiyimana ta sha suka kan karancin mai a ƙasar. Irina Inantore ta maye gurbin ta.[4]
Manazarta gyara sashe
- ↑ 1.0 1.1 Nadine Nkengurutse (24 February 2014). "Marie-Rose Nizigiyimana : le Commerce dans les mains d'une licenciée en Histoire" (in French). iwacu. Archived from the original on 20 May 2015. Retrieved 19 May 2015.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ "Burundi President reshuffles cabinet". Punch. 18 February 2014. Archived from the original on 20 May 2015. Retrieved 19 May 2015.
- ↑ Tom Odula (18 May 2015). "After coup attempt, Burundi President fire 3 ministers". The Washington Times. Retrieved 18 May 2015.
- ↑ "Burundian leader sacks defence minister". Premium Times. 18 May 2015. Retrieved 19 May 2015.