An haifi shehin malamin a birnin Sokoto ranar Litinin 13 ga watan Zulqidah shekara ta 1388 bayan Hijira, daidai da 2 ga Maris din shekarar 1969.

Ya yi karatun Ƙur'ani a gidansu a wajen mahaifiyarsa Modibbo Hafsatu, wacce ke da makarantar koyar da yara da matan aure.

Ya sauke Ƙur'ani yana da shekara takwas a lokacin yana aji uku na firamare.

Bayan sauke Ƙur'ani sai Ya fara karatun saniN Fiƙihu a wajenta inda ya karanta littattafai irin su Usul-din da Ishmawi da Ahlari.

Daga nan sai ya koma wajen mahaifinsa ya ci gaba da karatun Babus Sahwi ya kuma karatun Iziyya.

Bayan anaɗa mahaifinsa limancin ƙauyensu sai ya kasance ba ya samu lokacinsa, sai ya koma makarantar Malam Abbakar Makera Bakane.ya ci gaba da karatun Iziyya.

Daga bisani kuma ya koma wajen Malam Aliyu Muhammad Gidan Kanawa ya karanci littattafai irin su Riyadus Salihin da na Fiqihu kamar Risala, sannan ya kammala da Askari.

Ya kuma yi karatu a makaratantar Malam Muhammad Isa Talata Mafara ya karanta littattafai irin su Ihyaus Sunna da wasu littattafan Sheikh Dan Fodio da kuma wasu kamar Alburda da sauransu.

Malam ya yi karatu a wajen wasu malaman da dama. [1]

A ɓangaren boko ya yi firamare a makarantar Magajin Gari One, inda ya kammala a shekarar 1980, sai ya shiga makarantar sakandare ta Technical da ke Rinjin Sambo ya koyi fasaha da ƙere-ƙere.

"Ina iya cewa sau uku na yi sakandire saboda yanayin sauyin karatu," in ji malam.

"Bayan kammala karatu na je na samu horo a wani kamfanin motoci inda na fara aikin kanikanci har aka dauke ni aiki a UTC Kaduna a shekara ta 1985.

"Daga nan ne na samu gurbin karatu a Jami'ar Fasaha ta Minna don karantar ilimin kimiyyar komfuta da kuma wani gurbin a Kaduna Polytechnic, a cewar malam.

Sai dai sha'warsa ta koma wa karatun addinin Musulunci ta sa ya bar guraben inda ya ya koma makarantar marigayi Malam Bashir Yusuf a Talata Mafara.

Yana can ne sai ya samu gurbin karatu a Islamic African Center Khartoum da ke Sudan kan shari'a.

"Sai na ce ni makarantar sakandare nake son komawa, abin har ya zo ya zama rigima, da ƙyar aka amince. Wannan ya sa sau uku kenan ina yin sakandare daga SS1 zuwa SS3."

A shekarar 1990 sai ya samu gurbin karatu a Jami'ar Islamiyya Madina inda ya yi Kwalejin Hadisi daga shekarar 1990 zuwa 1994.

Daga nan ya komwa gida Najeriya ya fara aiki da KwalejinKimiyya ta jihar Sokoto a lokacin, State Poly kenan a yanzu, ya yi shekara biyu har da hidimar ƙasa, daga nan ya koma Jami'ar Usman Danfodi a shekara ta 1996.

Malam ya yi digiri na biyu da digirin digirgir a fannin Hadisi duk a Danfodio. Yanzu haka ya zama farfesa a ilimin Hadisi a watan Janairun 2019. [2]

Tambaya mai Sarkakiya

gyara sashe

Kamar yadda aka sani malamai kan Sha fama da amsa tambayoyi, to shi ma Farfesa Mansur haka abin yake gare shi.

"Ana samun tambayoyi masu sarƙaƙiya sosai. Sai dai ni ina da samun shakkar fatwa, idan har ina da shakku sai na ce a ban lokaci na yi bicike ko na tura wajen wani malamin.

"Akwai wata tambaya da aka min tun a shekarun 1990. Wasu matan aure su biyu mijinsu na zuwa ci rani Lagos. Gudar na da ilimi dayar kuma ba ta da shi.

"To lokacin babu waya mijin kan aiko da saƙo ne ta hanyar wasiƙa. Ita uwargida ita ce ta iya karatu ita ke karantawa idan an aiko saƙo.

"Rannan sai ya aiko da wasika uwargida na karantawa sai ta dubi amarya ta ce "me ki kai wa maigida ne?" Me ya faru ya sake ki saki uku?"

"Suka sha koke-kokensu amarya ta tafi gidansu ba wanda ya nemi ganin takarda. Ta yi zaman idda har ta yi aure.

"Mijin nan bai tashi zuwa Sokoto ba har sai da ta haifi yara biyu. Da ya dawo sai ya tarar amarya ba ta nan, ya gane abin da ya faru.

"To a gaskiyar magana da aka kawo batun wajena sai da na tura su kotu aka warware a can, don abin na da sarƙaƙiya da yawa," malam ya ce.

Farfesa ya ce ya tashi tare da 'yan da'awa. Yana hulda da su Adamu Badullahi da Malam Bello Dan Malam. Tun yana ƙaramar sakandare a shekara 13.

Ya buɗe makarantarsa ta farko a 1983, cikin ɗalibansa har da fitattun ƴan siyasa da manyan ƴan kasuwa.

Amma fara da'awa haƙiƙa sai bayan da ya kammala digiri a Jami'ar Madina bayan da ya buɗe makarantar Hadisi a gidansu. Makarantar na ci gaba har yanzu.

Ya ce "Na fara tafsirin Ƙur'ani a shiyyar Tsamiyar Dila."

Littatafai

gyara sashe

Malam ya rubuta littattafai da dama tun yana ɗalibi a Madina. Sannan ya rubuta cikin harshen Hausa da Larabci.

Wasu daga cikin na Hausan sun haɗa da:

Alkaki da Ruwan Zuma na tarihin Manzon Allah SAW Ƙaddara ta Riga Fata Abin da ya faru a Ƙarbala Aƙidun Shi'a a Ma'aunin Shari'a Su waye masoyan Ahlul Baiti? Duniya Makaranta Abokin hira Malam ya fi son abincin gargajiya musamman tuwon shinkafa da miyar kuka da kuma kwaɗon ƙanzo. [3]

Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-56115470
  2. https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-56115470
  3. https://www.bbc.com/hausa/rahotanni-56115470