Maƙoƙo
Maƙoƙo (Turanci: goitre) kumburi ne a cikin wuya sakamakon girmamar tsokar Tairod (thyroid).[1]. Ana iya alakanta Maƙoƙo da Tairod wanda baya aiki yadda ya kamata[2], inda yawa ko karancin zubar sinadarin Tairod a jiki kan haifarwa[3]
Maƙoƙo | |
---|---|
Description (en) | |
Iri |
thyroid gland disease (en) cuta |
Specialty (en) |
endocrinology (en) nuclear medicine (en) |
Medical treatment (en) | |
Magani | L-thyroxine (en) , methimazole (en) , propylthiouracil (en) , thyroglobulin (en) , triiodothyronine (en) da L-thyroxine (en) |
Identifier (en) | |
ICD-10-CM | E04.9 |
ICD-9-CM | 240.9 |
DiseasesDB | 5332 |
MedlinePlus | 001178 |
eMedicine | 001178 |
MeSH | D006042 |
Disease Ontology ID | DOID:12176 |
Fiye da kashi 90% na cututtukan na faruwa ne ta rashin sinadarin Aidin[4] Kalmar ta fito ne daga Latin gutturia, ma'ana makogwaro. Yawancin Maƙoƙo ba su da ciwon daji, ko da yake suna iya yin illa.
Alamomin Maƙoƙo
gyara sasheAlamomin Maƙoƙo sun hada da Kullun a gaban wuya, kusa da makogwaro, Jin matsewa a yankin makogwaro, kumburin jijiyar wuya, tari, Wahalar hadiya, Saurin bugun zuciya (tachycardia), zawo. zufa ba tare da motsa jiki ko ƙara yawan zafin jiki ba, da kuma girgiza[3].
Sanadi/Silar Maƙoƙo
gyara sasheA duk duniya, abin da ya fi zama sanadin goiter shine rashin sinadarin Aidin, wanda aka fi gani a ƙasashen da da kyar suke amfani da gishirin mai dauke da sinadarin Aidin. Ana kuma la'akari da ƙarancin sinadarin selenium a matsayin abin taimakawa. A cikin ƙasashen da ke amfani da gishiri mai dauke da siadarin Aidin, Hashimoto's thyroiditis (Maƙoƙon Hashimato) shine yafi kasancewa sanadi[5]. Maƙoƙo kan iya samuwa ta sanadin Gubar sayanaid (Cyanide), wanda ya zama ruwan dare a ƙasashe masu zafi inda mutane ke cin tushen rogo mai arzikin Sayanaid a matsayin babban abinci[6].
Bincike
gyara sasheAna iya gano cutar Maƙoƙo ta hanyar gwajin aikin Tairod (Thyroid function test), ga wanda dake zargin yana da shi[7].
Nau'ukan
gyara sasheAna iya rarraba ana iya rarraba Maƙoƙo kashi biyu, ko dai a matsayin Me-kololo nodular ko Me-yaduwa. Maƙoƙo Me-kololo ko dai na kololo ɗaya ne (uninodular) ko na kololo da yawa (multinodular[8]). Maƙoƙo Me-kololo da yawa shine yafi yawa gurin saka rashin lafiya na jijiyar Tairod[9].
wata cuta ce da take fitowa a wuyan mutum, takanyi kumburi sosai.[10]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Thyroid Nodules and Swellings". British Thyroid Foundation. 11 September 2019
- ↑ "Goitre - NHS Choices". NHS Choices. 19 October 2017
- ↑ 3.0 3.1 Can AS, Rehman A. Goiter (https://www.ncbi.nlm.nih.gov/books/NBK562161/). [Updated 2021 Aug 30]. In: StatPearls [Internet]. Treasure Island (FL): StatPearls Publishing; 2022 Jan-. Accessed 6/6/2022.
- ↑ Hörmann R (2005). Schilddrüsenkrankheiten Leitfaden für Praxis und Klinik (4., aktualisierte und erw. Aufl ed.). Berlin. pp. 15–37. ISBN 3-936072-27-2.
- ↑ Mitchell RS, Kumar V, Abbas AK, Fausto N (2007). Robbins Basic Pathology (8th ed.). Philadelphia: Saunders. ISBN 978-1-4160-2973-1.
- ↑ "Toxicological Profile For Cyanide" (PDF). Atsdr.cdc.gov. Archived (PDF) from the original on 28 July 2004. Retrieved 16 March 2017
- ↑ Goitre". nhs.uk. 19 October 2017. Retrieved 27 March 2019
- ↑ "Nodular Goiter - an overview | ScienceDirect Topics". www.sciencedirect.com. Retrieved 6 March 2022
- ↑ feingold, K. R.; et al. (2000). "Multinodular Goiter". MDText.com. PMID 25905424
- ↑ Blench, Roger. 2013. Mwaghavul disease names. Cambridge: Kay Williamson Educational Foundation.