ma'anar aure
Ma anar daurin aure

MA'ANAR AURE

gyara sashe

Aure wani zama ne halastacce tsakanin mace da namiji a matsayin mata da miji wanda al’ada da Addini suka yarda da shi. Babban dalilin da yasa ake yin aure shi ne domin yada iri tare da fatan al’umma ta wanzu. Aure baya inganta sai da rukunai kamar haka: sadaki, waliyi, shaidu.

Bisa wannan dalili, duk wanda ya ketare iyaka ya kutsa wata mace ba tare cika wadancan rukunai ba. Hakkka ya sabawa shari’a da kuma al’ada, saboda ladabtarwa shari’a tace ba aure. Al’ada ta bashi sunaye, sannan kuma ta kira aikin da ya yi da sunaye kamar haka: Za’a kira shi Kwarto, ya yi kwartanci, ko shige, ko fyade. Ita matar kuma a kira ta farka, ko dadaro. Matar da kuma ta sallamar da kanta ga kowa, ana kiranta karuwa. Shi kuwa dan ko da aka haifa ba ta hanyar aure ba, akan kira su da shege, ko shegiya, dan rariya, ko dan gaba da Fatiha, ko dan dakan-kuka da sauransu.

FALALAR YIN AURE

gyara sashe

Tabbas akwai falala a kan aure mara iyaka wadda ba za'a iya bayyana su ba sai dai a ɗan tsakuro kamar yadda shari’a ta kuma yi umarni da a yi aure tare da nuna muhimmancinsa, to haka ita ma al’ada ta bayyana falalar aure ga al’umma. Falalar aure da dan Adam ke samu sun hada da:-

1.Cikar mutunci 2.Natsuwa 3.Kamun kai 4.Runtse idanu 5.Yada zuriyya (haihuwa)

UMARNIN YIN AURE:  Bayan wannan falala kuma, sai maganar umarni da shari’a ta yi a kan yin aure a Al-}ur’ani aka ce: 

وإن خفتم ألا تفسطوا فى اليتامى فانكحوا ما طاب لكم من النساء مثنى وثلاث ورباع، فإنخفتم ألا تعدلوا فواحدة أو ما ملكت أيمانكم، ذالك أدنى ألاتعولو.

“Ku auri abin da ranku yake so daga bibbiyu, uku-uku, ko hur-hudu, in kunji ba za ku yi adalci ba, to ku tsaya a guda daya”. Abin nufi shi ne ku auri mata 2 ko 3 ko 4 in ba za ku iya adalci ba mata daya (1).

Wani hadisi yace ku yi aure ku hayayyafa ranar qiyama in yi alfahari da ku. Ko wani hadisin da yace: “Ku yi aure samari shi yafi runtse idanu.

GIRMAMA MACE SABODA MATSAYINTA

gyara sashe

Duk inda ka ga mace ka girmama ta saboda wasu dalilai kamar haka: matsayin da Allah Ya bata na Uwa ga dukkan mahaluki kuma makarantar farko ga dukan mahaluki. 1. Matar wani 2. Uwar wani 3. Kakar wani.

Da farko dai ya zama wajibi a girmama mace bisa wasu dalilai, na farko shi ne duk in da ka ga mace kamila to dole ne ta kasance cikin dayan uku ko dai matar wani ko uwar wani ko kakar wani, ko da yake wannan na karshe ya danganci shekarunta.

عن أنس رضى الله عنه قال: قال النبى صلى الله عليه وسلم قال: إذا تزوخ العبد فقد استكمل نصف الدين, فليتق الله فى النصف الباقى. An karbo daga Anas (R.A) yace Annabi (S.A.W) ya ce idan mutum ya yi aure to ya sami rabin Addinin sa sauran rabin sai ya ji tsoron Allah ya cika sauran. (Jami’ul hadis: Imamus-suyuɗi).

GIRMAMA MACE A MATSAYIN MATAR AURE

gyara sashe

Akwai dalilai masu yawa da suka sa mutum dole zai girmama mace ko ba don komai ba, ko saboda wani matsayi da take da shi a al’umma na farko a matsayin matar aure, wani babban mataki ne na rayuwa ga duka dukkan namiji. Babu wani wanda rayuwar sa za ta kammala in ba shi da aure.

To ashe kuwa in har haka ne to mace ta zama abokiyar rayuwa, kuma abokiyar rufin asiri ga mai ita. Wata hujja itace Allah (S.W.T) yace a cikin Al-qur’ani cikin Suratul Bakara aya ta 237 ya ce miji da mata tufa ne ga juna, sannan yace a Suratul Bakara aya ta 228, 29-30 cewa mata da miji a yi karamci ga juna. Bayan wannan kuma, irin gudunmuwar da mace take bayarwa a fagen aure wanda ba za su lissafu ba, kadan daga ciki sun hada da:

1- Kula da miji shi kansa. 2- Kula da gida da iyali. 3- Karewa da karawa mutum mutunci a cikin al’umma. 4- Tsare kai daga fadawa cikin wasu munanan ayyuka. 5- Runtse idanunsa daga wasu matan daban. 6- Taimakawa wajen samun zuriyya (yaɗa iri). 7- Matar kwarai na sanya miji ya yi alfahari. 8- kulla zumunci da sauransu.

Wani sirri kuma abin mamaki game da dangantakar aure, ga ma’auratan nan biyu. Watau mata da miji, shi ne kula da juna musamman aka ce auren farko tsakanin saurayi da budurwa. Matukar an yi shi bisa so da kauna kuma an amincewa juna. To za ka iske babu mai son ya rabu da juna, domin samun kulawa. Akwai wata magana da masana dabi’ar dan Adam suka yi na cewa duk wanda ya rasa matar farko ko mace ta rasa mijin farko to da wuya ya/ta sake samun dai-dai sai kawai haluri.kai ko da wajen ba shi shawara mai kyau.

A mafi yawan lokutta akan samu a inda mata ke kula da miji kuma har ta rinka lallashi da tattalinsa da kayansa kamar danta ko na karamin yaro ko da baya nan kuwa. Ban da wannan kuma, mata kan kula da gida tare da iyali kai a wani lokaci har da dangi. Tun daga yi mu su abinci raino, tsabtar jiki da ta tufafi (wanka da wanki) tarbiyya.

Mace ga mijinta takan zama kyaure da kuma ado ko garkuwa ta mtunci a cikin al’umma. Game da wannan babu jayayya bisa ga wasu dalilai kamar haka: ko ba shari’a a dabi’a ma kawai ya isa hujja a mutane musamman Hausawa matuƙar aka ce ga namiji ya kai wani matsayi na minzalin isa aure aka ce bai yi ba, har suna akan bashi da cewar “tuzuru”, ko “gwadankwarƙi”,/”goriyo”, shi kuwa wanda matar ta fita watau ya taba yin aure amma suka rabu to shi akan kira shi da “gwauro”. Haka ita ma macen akan ce “karfa” ko kuma ta rabu mijin a ce “bazawara” ko a tsokaneta da “gwauruwa”.

Wata daraja da Allah (S.W.T) ya baiwa matar aure ga miji ba karama ba ce, saboda falalar da miji kan samu a dalilin yin aure, kamar a inda wani hadisi ya nuna ko da kallon fuskar matarsa kawai ya yi, za a rubuta ma sa lada. Ga hadisin kamar haka: “An karɓo daga Abu Hurairah (R.A) cewa: Ya ji Manzon Allah (S.A.W) idan namiji ya dubi fuskar matarsa, Allah (S.W.T) zan rubuta masa ladan kyawawan ayyuka guda dari a cikin littafinsa na lada, idan ya kama hannunta, kuma ya sadu da ita, Allah Zai rubuta masa lada a kan kowanne silin gashin da ke jikinsa, idan ya yi wankan janaba Allah Zai halicci Mala’ika a kan kowanne digon ruwan da ya diga a kasa a lokacin da yake yin wankan. Kowane Mala’ika zai rinka yi wa Allah tasbihi, kuma yana roka masa uban giji tun daga wannan lokacin da ya yi wankan har zuwa ranar lahira. Kuma ladan dukkan tasbihin da Mala’ikun za su yi za a rubuta masa ne a cikin littafinsa na lada. Idan matar ta yi sa a ta dauki ciki a wannan saduwar, dukkan mala’ikun da ke cikin Al’arshi da kifayen dake cikin ruwa za su rinka roka masa lahira gurin ubangiji. Ita matar kuwa za a rinka rubuta mata lada guda dubu a kankare mata zunubai dubu, kuma a bata ladar da mutane suka fita yaki (jihadi).

ZABARWA YAYA UWA TA GARI

gyara sashe

Wajibi ne ga dukkan mahaluki mai hankali da yayi niyyar yin aure, to ya yi kokarin zaɓarwa yayansa uwa ta gari, ma'ana mai tarbiyya da son addini. Kar ya bi son zuciya ya auro mace don kyau, watau kyakkyawa, ko Yar wane, watau mai nasaba (mai kudi, sarauta, mukami). Wannan magana ta yi dai-dai da wani bayani da Manzon Allah (S.A.W) ya yi cewa ku auri mace ma'abuciyar addini. Domin yace in ka aura don kyau to lallai kyau kan Kare in ta tsufa, ko nasaba don mulki na iya karewa, amma shi addini ba ya karewa.

Bayan haka, zabarwa yaya uwa ta gari kamar hutar da kai ne, domin in ka haifi yara da mace ta kwarai. To kamar ita ce makarantar su don zasu koyi komai na kwarai daga wurinta. Saboda masu hikima sun ce uwa itace makarantar farko ga yaro. Haka kuma in mutum ya kurkure ya auri Ballagazar mace mara tarbiyya, To ya kashe kansa da kansa, kuma yaransa sun shiga uku.

Babban dalili shi ne, ita ba ta da tarbiya, ba ilimi balle addini, to a nan ina makarantar farko take? Sai dai su koyi zagi da miyagun halaye.

KOWA NA DA HAKKIN DA YA RAYATA A WUYANSA.

gyara sashe

Akwai Hakkin na kasa ko karami ko mai rauni ko talaka, akan na sama, shugaba, iyaye da duk wani jagora. Wajibi ne a tsare-tsare da lura da wadannan Hakkoki ta kowacce fuska. Wani hadisi wanda Bukhari da Muslim suka ruwaito, wanda yayi bayani a kan cewa duk wani jagora akan al'amari to lallai ne ya tsare amana da aka bashi. Domin kuwa za a tambaye shi ranar lahira. Ga yadda hadisin yake kamar haka:- وعن ابن عمر رضى الله عنهما قال: سمعت رسول الله صلى الله علسه وسلم يقول: كلكم راع, وكلكم مسئول عن رعيته, ألإمام راع, ومسئول عن رعيته, والجل راع فى أهله ومسئول عن رعيته, والمرأة راعية فى بيت زوجها, ومسئولة عن رعيتها, والخلدم راع عن مال سيده ومسئول عن رعيته, فكلكم راع, ومسئول عن رعيته. متفق عليه. رواه البخارى و مسلم. An karbo daga Ibn Umar (R.A) yace: Naji Manzon Allah (S.A.W) yace: "Dukkan ku makiyaya ne, kuma dukkan ku abin tambaya ne a kan abin da aka bashi kiwo. Shugaba abin tambaya ne a kan na karkashin sa. Kowane mutum mai kiwo ne a kan iyalan sa, kuma abin tambaya ne, ita kuma mace mai kulawa ce a kan dukiyar (gida) mijinta, kuma abin tambaya ce a kan su. Mai yin hidima (bara), mai kulawa ne ga dukiyar uban gidansa, kuma abin tambaya ne a kan su. Dukkan ku makiyaya ne kuma abin kulawa ne. An yi ittifaki a kan wannan hadisin. (Bukhari da Muslim suka ruwaito shi).

Shari'ar musulunci ta tsoratar da cewa duk wanda ya take Hakkin wani dan'uwansa na kusa ko nesa, musulmi ne ko wanda ba musulmi ba? Kai hatta dabbobi su ma an yi hanin a cutar da su haka kurum. Haka kuma shari'ar musulunci ta kwadaitar tare kuma da yin albishir ga duk wani mahaluki da ya tsare tare da sauke Hakkin wani da yake kansa, baya ga tarin lada da falala da kauna da zai samu a nan duniya, sannan kuma ga tanajin gidan aljannah. Misali a cikin Al-}ur'ani a cikin Suratul Zilzilat inda Allah (S.W.T) yace: فمن يعمل مثقال ذرة خيرا يره. "To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarrah, na alheri, to zai gan shi". ومن يعمل مثقال ذرة شرا يره. "Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarrah na sharri, zai gan shi".

HAKKIN MATA A KAN MIJINTA

gyara sashe

Matar aure da na Hakkoki masu yawa da suka zama tilas mijinta da yake aurenta ya tsare su. Tun daga farko dai shari'a ta shardanta babu aure sai da abubuwa uku, sune waliyyi, sadaki, sai kuma shaidu. Daga cikin wadannan abubuwa guda uku to daya shine mafi karfi a cikinsu a matsayin Hakkin na ita matar, shi ne sadaki, domin kuwa wajibi a baiwa mace sadakin ta a hannun ta, ko kuma a saya mata wani abu muhimmi wanda za ta rinƙa amfani da shi.

Bayan wadannan kuma, sai maganar wasu Hakkokin kuma, bayan an daura aure, wajibi ne miji ya tsare su, sune ciyarwa, shayarwa, tufatarwa, dakin kwana, sannan da biya mata bukata wajen kwanciya. Matukar aka rasa daya daga cikinsu, to ana iya raba aure.

Bisa ga maganar magani kuwa, baya cikin sharaɗin aure, cewar mutum ya yi wa matarsa magani ba ta da lafiya, sai dai in ya yi mata maganin to ya kyautata, amma ba dole ba ne. Sai dai kuma malamai sun yi Ijtihadin cewar in miji ya yi wa matarsa magani to ya kyautata, haka ita ma ba dole ne ta yi masa girkin abinci ba, amma in ta yi to ta kyautata.

An karɓo daga Amru Ɗdn Ahwas, Aljushami (R.A), yaji Annabi (S.A.W) a hajjinsa na bankwana bayan ya yi yabo da godiya ga Allah, kuma ya yi wa'azi, kuma ya yi gargadi, sannan yace: "Ku saurara! Ku karbi wasiyyar alheri dangane da al'amarin mata, lallai su (mata) kamar kamammu ne, a wurinku baku mallaki komai ba a kan su in ban da (igiyar aure), sai dai in sun zo da alfasha bayyananniya. Idan sun aikata (alfasha), ku kaurace musu a wurin kwanciya, ku buge su duka ba mai tsanani ba. Idan suka yi muku biyayya kada ku nemi wata hanyar kama su da laifi."

"Ku saurara! Lallai kuna da hakki a kan matan ku, kuma matanku suna da hakki a kan ku. Hakin ku a kan su shi ne kada su zaunar da wanda baku so a kan shimfidar ku, kuma kada suyi wanda baku so izinin shiga gidajen ku. Ku saurara! Hakkin su a kan ku shi ne ku kyautata musu, tufatarwa da ciyarwa." Imam Tirmiziy ya ruwaito.

An karɓo daga Mu'awuya dan Haida (R.A) yace: Ya Manzon Allah! Mene ne Hakkin matar Ɗayan mu a kan sa? Sai yace: "Idan ka ci, kaciyar da ita, ka tufatar da ita idan ka tufatu, kuma kada ka doke ta a fuska, kuma kada ka musguna mata, kuma kada ka kaurace mata sai a cikin daki."

An ruwaito daga Abdullahi Dan zama'a (R.A) cewa: Annabi (S.A.W) yayi wa'azi dangane da al'amarin mata, yace yanzu dayanku zai tasarwa matarsa ya yi mata duka irin dukan bawa, sannan kuma idan dare ya yi ya kwanta da ita? Bukhari da Muslim suka ruwaito.

HAKKIN MIJI A KAN MATARSA

gyara sashe

Akwai hakki mai nauyi kuma mai girma da miji ke da shi a kan matarsa wanda ya shafi na girmamawa na, bin umarni ko hani. Hakkin biyayya ga miji ba karamin al'amari ba ne, saboda ko da sha'awa ta taso wa miji in ya bukaci matarsa to dole ne ta masa kira, domin kuwa matukar taki to lallai za ta shiga fushin Allah, saboda in har mijinta na fushi to sai ta bashi haƙuri sannan za ta kuɓuta. وعن أبى هريرة رضى الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: إذا دعا الرجل امرأته إلى فراشة فلم تأته فبتا غضبان عليها العنتها الملائكة حتى تصبع. متفق عليه. An karɓo daga Abu-Hurairah (R.A), yace Manzon Allah (S.A.W) yace: Idan miji ya kira matar sa zuwa shimfiɗarsa, watau ya nufi ya kwanta da ita amma ta ƙi, ma'ana ta ƙi yarda da shi, har shi mijin ya yi fushi da ita, Mala'iku zasu yi ta tsine ma ta har zuwa asuba. Bukhari da Muslim suka ruwaito.

فى رواية قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: والذين نفسى بيده ما من رجل يدعوامرأته إلى فراشة فتأبى غليه إلاكان الذى فى السماء ساخطا عليها حتى يرضى عنها. A wata ruwayar, an ce Manzon Allah (S.A.W) yace: Na rantse da wanda raina ke hannun sa, babu wani miji wanda zai kira matar sa zuwa shimfiɗarsa don su kwanta amma ta ƙi, har sai waɗanda suke sama (Mala'iku) sun yi fushi da ita har sai ya yafe ma ta.

Akwai wani hadisi ya ƙara nuna ƙarfin yin biyayya ga miji, kamar inda Manzon Allah (S.A.W) ya ce da zan yi umarnin wani ya yi wani sujada da na umarci mata ta yi wa mijinta sujada. Bayan wannan kuma akwai wani hadisi kuma da yake nuna matsayin haƙƙin miji kamar inda aka yi bayanin cewa Aljannar mace tana ƙarƙashin duga-dugin mijin ta in ta bi shi, ta shiga Aljannah.

Bugu da ƙari, akwai inda aka nuna cewa ko da ibada ce mace za ta yi, sai ta nemi izinin mijin ta, kamar misalin azumin nafila, hadisi ya nuna cewa ta sanar da miji, ko ta nemi izini sannan ta ɗauka. Duk dai a kan nuna girman biyayya ga miji, inda aka nuna ko da mace tana tuya gurasa ko waina, in har miji ya nuna yana buƙatar ta, wato sha'awa, manufa yana so ya kwanta da ita, to dole ta amsa kira, ta je su kwanta, ya biya buƙatarsa ko da kuwa gurasar ko wainar za su ƙone.

Akwai bayani da ya zo da ya nuna a lokacin Manzon Allah (S.A.W) yana raye a zamanin wata matar wani sahabi ya yi tafiya sai aka aiko cewa mahaifin ta bashi da lafiya, don haka sai ta aika tana neman izini daga wurin Annabi (S.A.W) don ta tafi ta dubo shi, Annabi yace shin mijin ta ya bata izini? Sai tace a'a, sai yace to ta haƙura. Bayan haka sai kuma aka aiko cewa mahaifinta ya rasu, duk da haka ba ta fita ba, ta haƙura har sai da mijin ta ya dawo. A kan wannan ne Annabi (S.A.W) ya aiko cewa an sanar da shi cewa an gafarta wa mahaifinta, saboda biyayyar da ta yi, duk da mijin ta baya nan, kuma ta haƙura har ya dawo.

BIYAYYA GA MIJIN TA

gyara sashe

Biyayyar mace ga mijinta wajibi ne, saboda wani hadisin da Annabi (S.A.W) yai umarni cewa: Da mutum zai iya yiwa wani mutum sujada da an umarci mata ta yi wa mijinta sujada. To amma da yake ba zai yiwu ba, ba a yi wa kowa sujada sai Allah (S.W.T), amma shari'a ta yi umarni mace ta yi wa mijin ta biyayya matuƙar dai bai umarce ta da ta yi saɓon Allah ba.

Da Wani Zai Iya Yiwa Wani Sujada, DaMata Ta Yi Wa Mijin Ta. وعن أبى هريرة رضى الله عنه، عن النبى صلى الله عليه وسلم قال: "لوكنت أمرا أحدا أنيسجد لأحد، لأمرة المرأة أن تسجد لزوجها. رواه الترمذى حديث حسن صحيح. An karɓo daga Abu hurairah (R.A), daga Manzon Allah (S.A.W) yace: Da mutum zai iya yiwa wani mutum sujada da an umarci mata ta yi wa mijinta sujada. Tirmiziy ne ya ruwaito shi.

MACE BA ZA TAYI AZUMIN NAFILA BA SAI DA IZININ MIJIN TA

      وعن أبى هريرة رضى الله عنه أيضا، أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال:لايحل لأمرأة أن تصوم وزوجها شاهدا إلا بإذنه، ولا تأذن فى بيته إلا بإذنه. متفق عليه، وهذا لفظ البخارى.

An karbo daga Abu hurairah (R.A) yace: Manzon Allah (S.A.W) yace: "Bai halatta ba ga mace ta yi azumin nafila ba kuma mijin ta na nan, sai da izinin sa. Kuma ba za ta shigar da wani cikin gidansa ba sai da izinin mijinta. Bukhari da Muslim suka ruwaito.

HAƊARIN BUTULCEWA MIJI. عن ابن عساكر، عن عائشة رضى الله عنهما: قال النبى صلى الله عليه وسلم: إذا قالت المرأة لزوجها ما رأيت منك خيرا قط فقد حبط عمنها.

An karbo daga Dan Askar, daga Aisha (R.A) tace: Annabi (S.A.W) yace: "Duk macen da ta cewa mijinta bata taba ganin alheri daga wurin sa ba, to hakika ta bata ayyukan ta.

ADADIN MATAN ZA A IYA AURA

gyara sashe

A tsari irin na shari'ar musulunci, ba a bar komai haka ba, sai da aka yi masa iyaka tare da ka'idoji. A kan wannan ne, aure ma ba a bar shi haka ba, sai da aka shimfida ka'idoji da hukunce-hukunce. Allah (S.W.T) a cikin Al-qur'ani ya kayyade ko iyakance adadin mata da za a iya aura tun daga mata biyu ko uku ko huɗu, amma sai aka yi gargaɗi in mutum ya san ba zai yi adalci a tsakanin matansa ba, to ya auri mace ɗaya.

وإن خفتم ألا تفسطوا فى اليتامى فانكحوا ما طاب لكم من النساء مثنى وثلاث ورباع، فإنخفتم ألا تعدلوا فواحدة أو ما ملكت أيمانكم، ذالك أدنى ألاتعولو. MATAN DA SUKA HALASTA A AURA

Allah (S.W.T) ya baiwa mata wani irin matsayi a karkashin inuwar shari'ar Musulunci, wanda babu wani tsari da aka taba samu a kafin musulunci da kuma nan gaba. Wannan irin matsayi ya sanya dole a girmama mata.

Allah (S.W.T) cikin hikimar sa ya halasta yin aure, to amma duk da haka, sai ya tsara mata kashi biyu, kashi na farko ya haramta aurensu ga dukkan mutum musulmi, kashi na biyu kuwa wadanda basu fada cikin wadancan da aka ambata ba da farko, ya halasta su, watau za a iya auren su.

MATAN DA SUKA HARAMTA A AURA

gyara sashe

Shari'ar musulunci ta haramta auren wasu mata ga musulmai maza. Wannan haramci ya dogara ne bisa ga wasu dalilai, sannan kuma an kasa kashi hudu kamar haka:- 1- Akwai mata wadanda dangantaka ta jini (haihuwa). 2- Akwai mata wadanda alakar auratayya ta hana (surukai). 3- Akwai mata da alakar shayarwa ta hana (marikiya). 4- Akwai mata da sabanin addini ya hana (mushirikai).

1. Haramci a dalilin nasabar jini (haihuwa).

a. Kaka (mahaifiyar uwa ko uba.

b. Uwa.

c. Inna (yar uwa, kanwar uwa).

d. Gwaggo (Yar uba, kanwar uba)

e. Yar tsatso.

f.

. JikanyG. g. Yar jia. h. Yaya da Yayansa mata. i. Kanwa da yayanta mata.

2. Haramci a dalilin auratayya. a. Matan uba (kishiyoyin uwa). b. Uwar mata (Suruka). c. Diyar mata (agola). d. Matar ]a (suruka). e. Kanwar ko Yar mata (idan tana da rai), ba a haɗa su a lokaci daya.

3. Haramci a dalilin shayarwa (raino). a. Matar da ta shayar da mutum nonon ta. b. Ya'yan ta.

4. Haramci a dalilin sabanin Addini (wadanda ba musulmi ba, ba kiristoci ba, ba Yahudawa ba). a. Maguzawa. b. Riddaddu (wadanda suka yi ridda). c. Matsafa.

HARAMCIN kAURACEWA MIJI A SHIMFIDA

gyara sashe

Shari'ar Musulunci ta yi hani ko haramta mace ta kauracewa mijinta a shimfida, watau lokacin kwanciya in ya bukaceta, ma'ana ya kirata saboda haka zata shiga fushin Allah, mala'iku zasu yi ta tsine mata har sai gari ya waye. وعن أبى هريرة رضى الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: إذا دعا الرجل امرأته إلى فراشة فلم تأته فبتا غضبان عليها العنتها الملائكة حتى تصبع. متفق عليه.

An karbo daga Abu-Hurairah (R.A), yace Manzon Allah (S.A.W) yace: Idan miji ya kira matar sa zuwa shimfidarsa, watau ya nufi ya kwanta da ita amma ta ki, ma'ana ta ki yarda da shi, har shi mijin ya yi fushi da ita, Mala'iku zasu yi ta tsine ma ta har zuwa asuba.Bukhari da Muslim suka ruwaito.

JIRWAYEN AURE A ADABIN BAKA

Tabbas an samu jirwayen jigon a adabin bakan Bahaushe, musamman a rassansa guda biyar. Kamar Karin Magana, da take da kirari, da tatsuniya, da almara, da maganganun azanci da sauransu.Wannan ya Kara nuna matsayin aure a al’adar Bahaushe.

KARIN MAGANGANU: Game da karin maganganu a kan aure da al’adar Bahaushe ta yi, suna da yawa, kamar haka: 1- Idan da rai saurayi ma Ango. 2- Da kamar wuya tsohuwa da auren nesa. 3- Yakamata auren na gida. 4- Amarya ba kya laifi ko ta kashe danmasu gida. 5- Ango hana gada. 6- Ango baka ji asalatu. 7- Allah ya yi aure da mara wuri(kudi). 8- Biki na farar kaza belbela ba gayya ba. 9- Biki wan shagali. 10- Biki-biki da zani kowa ya raina biki ba nashi ba ne.

KIRARIN AURE: Game da kirarin aure da al’adar Bahaushe ta yi, suna da yawa, kamar haka:

1.Aure jibadau kayan nauyi. 2.Auren fari na dakushe haukar balaga duk wanda aka yi wa zai yi hankali. 3.Auren fari dabaibayi ga tuzuru. 4.Aure Yakin yanmata. 5. Na guga marmari daga nesa. 6. Aure kafi karfin yaro.

IRE-IREN AURE

gyara sashe

Aure dai kalma daya ce manufa daya, sai dai kuma yana da rabe-rabe kamar kashi goma sha biyu. Duk da rabe-raben zaka samu kudurin su daya ne, ko da za a samu bambanci, sai dai kadan abin da ba a rasa ba.

Don kuwa zaka sami mata da miji suna kaunar juna da girmama juna ko da haihuwa ko babu. Muna da aurarraki kamar haka: - 1- Auren Kudi.(wanda aka biya sadaki, da sauran dawainiya.) 2- Auren Sadaka.( wanda aka sadaukar da sadakin) 3- Auren Zumunci.(aure na Yan uwa, dangin uwa ko na uba.) 4- Auren Dole/ƙi.(an yi bisa tilas, ko ango, ko amaryar wani bai so.) 5- Auren dauki sandar ka/takalmi.(a auri mace tana gidanta daban) 6- Auren Jeka da kwarinka.(a auri mace tana wani gari daban.) 7- Auren Jari.(a auri mace saboda kudinta ko na iyayanta.) 8- Auren daukar buta.(auren tsoho da tsohuwa,don ta zuba mai ruwa). 9- Auren boyon wata.(auren da akan yi kafin azumi, in ya wuce a fita). 10- Auren kashe wuta.(auren da akan yi don a koma gun tsohon miji). 11- Auren huce takaici.( auren da akan yi don a share hawaye) 12- Auren kangara. (auren da masu arziki kan yi, a tayar baikon wasu).

TATSUNIYA:Akwai tatsuniyoyi da dama da aka samu jirwayen jigon aure a a cikinsu.misali: 1.Tatsuniyar Barewa ta auri mutum. 2.Tatsuniyar auren gaurakiya da biri. 3.Tatsuniyar shaida kurciya. 4.Tatsuniyar kaza ta mazuru. 5.Tatsuniyar Gizo da koki.

KAMMALAWA

gyara sashe

A ƙarshe wannan mukala ta tabo, wani abu da ya shafi rayuwar aure da matsayinsa. Haka nan an nazarci matsayin aure da muhimmancinsa ga dukkan wani abu mai rai. Tun daga mutum har dabbobi, da tsuntsaye, kwari, da tsirrai. An kuma fito da dalilai da suka sanya Bahaushe ya bai wa aure babban matsayi. An bayyana yadda Bahaushe ke kallon duk namijin da ya rika (balaga), ma’ana ya isa aure amma bai yi ba, a matsayin mai rauni kuma ba cikakken mutum ba. Bugu da ƙari kuma, an kawo yadda Bahaushe ya karkasa mutane marasa aure zuwa gida uku ko hudu. Kowane daga cikinsu akwai irin matsayinsa a al’adar Bahaushe, tare da dalilai da suka sa aka bashi suna. Haka kuma, an kawo falalar dake tare da aure, sannan ga jirwayen adabin bakan Bahaushe da sauransu.

Domin haka,ina fatan wannan muƙala, ta zama kamar matashiya ce ga masu hankali daga cikinmu maza da mata.

A SuyuɗI Jami’ul Hadisi.

Bargery G.F.(1993)A Hausa-English Dictionary English-Hausa Vocabulary Ahmadu Bello University Zaria

Yaro Y.I.(1971)Tatsunniyoyi da Wasanni.Oxford University Press, Ibadan.

S.Aliyu (2001) Addu’a’u min kibabi was’sunnah Maktabatu Anwaru Abdullahi, Kurmi Market, Kano.

Abdullahi Fodiyo( )Sabiblil Najati. Jafaru Bin Alhaji, Hussaini Alkamawa Sakkwato.

Zaid A.A Risala Fassarar Hausa. Kurmi Market, Kano.

Gumi A M. (1980) Al-qur’ani mai girma,Tarajamar Hausa.

Hadimil haramaini, Sharifaini Makkah.

Malik I.(1970) Muwadda Malik. Darul fikri, Beirut Lebanon. Annawawi I. Riyadus salihin. Darul fikri, Beirut Lebanon.

Ladan Y.(1980)Zaman Duniya Iyawa ne.Northern Nigerian Publication Company, Zaria.

East R.(1966)Ikon Allah (Dabbobi). Northern Nigerian Publication Company,Zaria.

Imam Z.( )Kitabul Kaba’ir, Darul fikri, Beirut Lebanon.