Lindiwe Chibi
Lindiwe Chibi (1976–2007), ƴar wasan kwaikwayo ce ta Afirka ta Kudu. Ana yi mata kallon ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasan kwaikwayo a gidan talabijin na Afirka ta Kudu, an fi saninta dalilin rawar da ta taka a matsayin 'Doobsie' a cikin fitaccen fim ɗin Muvhango.
Lindiwe Chibi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Afirka ta kudu, 1976 |
Mutuwa | 2007 |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi da ɗan wasan kwaikwayo |
Harbin bindiga da Mutuwa
gyara sasheA ranar 30 ga watan Afrilu 2005, saurayinta Dan Mokoena, ya harbe ta a fuska lokacin da Chibi ke gidan mahaifiyarta.[1] Harbin da aka harba a kusa, ya shiga kumatu kuma ya fita ta bayan kanta. Cikin gaggawa an Kaita asibitin Garden City Clinic ta kasance acan na ɗan makonni. Bayan tashi daga coma, ta gurgunta a gefen dama na jikinta. lokacin da ta warke daga mummunan rauni, ta mutu daga cutar huhu a asibitin Chris Hani-Baragwanath da ke Soweto a 2007 tana da shekaru 31 a duniya.[2]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "'Doobsie' written out of soapie". news24. Retrieved 2020-11-30.
- ↑ "Throwback: South African soap stars who died in real life". all4women. Retrieved 2020-11-30.