Linda Spilker ƙwararriyar yar kimiya ce ta duniya wacce ta yi aiki a matsayin ƙwararren masaniyar kimiyyar aikin Cassini da ke binciken duniyar Saturn . Abubuwan bincikenta sun haɗa da juyin halitta da haɓakar zoben Saturn.

Linda Spilker
Rayuwa
Haihuwa Tarayyar Amurka, 1955 (69 shekaru)
Karatu
Makaranta California State University, Fullerton (en) Fassara
University of California, Los Angeles (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Ilimin Taurari
Employers Jet Propulsion Laboratory (en) Fassara
IMDb nm1995978

Spilker ta sami B.A.in Physics daga Jami'ar Jihar California, Fullerton a cikin shekara 1977 da MS a cikin Physics daga Jami'ar Jihar California, Los Angeles a 1983. Ta samu Ph.D. a cikin Geophysics da Space Physics daga UCLA a cikin shekara 1992. Ta shiga dakin gwaje-gwaje na Jet Propulsion Laboratory a shekara 1977, da farko tana aiki a kan ayyukan Voyager da aka kaddamar a wannan shekarar. Ta zama masaniyar kimiyar Cassini shekara 1990. A cikin shekara 1997, ita ce editan littafin NASA wadda ta taƙaita abubuwan da aka daga manufarta. A cikin shekara 2010 ta zama masaniyar kimiyyar aikin Cassini, rawar da ta jagoranci duk binciken kimiyyar ƙungiyar. Ta fito a matsayin kanta a cikin shirye-shiryen talabijin da yawa, gami da da yawa a cikin jerin PBS Nova.

Girmamawa da kyaututtuka

gyara sashe
  • Medal na Musamman na NASA shekara (2013)
  • Kyautar Nasarar Ƙungiya ta NASA shekara (2011, 2009, 2000, 1998, 1982-1989)
  • Kyautar Nasarar Kimiyya ta NASA shekara (1982)

Duba kuma

gyara sashe
  • Jerin mata masu matsayi na jagoranci akan ayyukan kayan aikin taurari