Oba Sir Ladapo Samuel Ademola, KBE, CMG (1872–1962), wanda aka fi sani da Ademola II, shi ne Alake na Abeokuta daga shekara 1920 zuwa 1962. Kafin a nada shi Alake, Ademola yana da hannu a cikin harkokin gwamnatin Egba United Government. A matsayinsa na dan majalisar Egba, 'ya kasance jigo a tattaunawar da aka yi da gwamnatin mulkin mallaka na jihar Legas a shekarar 1889 don yancin gina titin jirgin kasa da ya ratsa ta Egbaland.[1] A 1904 ya yi tafiya tare da Alake Gbadebo zuwa Burtaniya, inda Sarki Edward VII 'ya tarbe su. Ya gaji Oba Gbadebo a shekarar 1920 da kuri'u masu, yawa daga majalisar Egba.

Ladapo Ademola
Rayuwa
Haihuwa Abeokuta, 1872
Mutuwa 27 Disamba 1962
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Ladapo Ademola

Manazarta

gyara sashe
  1. The Christmas number of the Nigerian Daily Times, 1932. (1932). Lagos, Nigeria: W.A. P. 8