Laburaren Ƙasa Na Tunisiya
Laburaren ƙasa na Tunisiya (Larabci: المكتبة الوطنية التونسية ) shine ɗakin karatu na haƙƙin mallaka na doka na Tunisiya. An kafa shi a cikin shekarar 1885, wanda aka fi sani da Laburare na Faransa, sannan kuma ɗakin karatu na Jama'a. Gwamnatin Tunisiya ta ware kasafin Dinare miliyan 28 don gina sabon ginin ɗakin karatu, kuma a shekara ta 2005 an mayar da ɗakin karatu wurin. [1] Laburaren yana da tsayin mita 70 kuma ya kunshi benaye 14 yana daya daga cikin manyan gine-gine a kasar Tunisiya kuma daya daga cikin gine-ginen da aka fi sani da tsarin Musulunci a kasar Tunisia.[2]
Laburaren Ƙasa Na Tunisiya | |
---|---|
| |
Bayanai | |
Iri | national library (en) |
Ƙasa | Tunisiya |
Mulki | |
Hedkwata | Tunis |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1885 |
|
Tarihi
gyara sasheAn kafa wannan ɗakin karatu a cikin shekarar 1885, ana kiran wannan ɗakin karatu na Faransanci. Sunanta na yanzu tun daga farkon samun 'yancin kai na Tunisiya. A cikin shekarar 2005, an sake komawa wurin da yake yanzu, Boulevard 9 avril, kusa da National Archives na Tunisia da wasu manyan cibiyoyi kamar Faculty of Social and Human Sciences.[3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ " ﺍﻟﻤﻜﺘﺒﺔ ﺍﻟﻮﻃﻨﻴﺔ ﺍﻟﺘﻮﻧﺴﻴﺔ ﻣﻜﺴﺐ ﻣﺘﻤﻴﺰ ﻟﻠﺜﻘﺎﻓﺔ ﺍﻟﻌﺮﺑﻴﺔ ﻭﺍﻹﺳﻼﻣﻴﺔ " [The National Library of Tunisia, a triumph for Arab Islamic culture] (in Arabic). Turess Tunisia. 2 November 2009. Retrieved 15 November 2021.
- ↑ Marcel Lajeunesse, ed. (2008). "Tunisie". Les Bibliothèques nationales de la francophonie (PDF) (in French) (3rd ed.). Bibliothèque et Archives nationales du Québec . OCLC 401164333 .
- ↑ "Tunisia" , World Report 2010 , The Hague: International Federation of Library Associations , OCLC 225182140 , "Freedom of access to information". (Includes information about the national library)
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Shafin hukuma (in English, French, and Larabci)