Kwalejin Malamai ta Adeniran Ogunsanya
Kwalejin Malamai ta Adeniran Ogunsanya | |
---|---|
| |
Knowledge, Culture and Service | |
Bayanai | |
Iri | cibiya ta koyarwa |
Ƙasa | Najeriya |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1958 |
aocoed.edu.ng |
Kwalejin Malamai ta Adeniran Ogunsanya, wanda aka fi sani da AOCOED, ita ce kuma cibiyar ilimin gaba da sakandare da ke yankin al'ummar Oto-Awori a yankin Oto-Awori na Ojo, Jihar Legas.[1] Kwalejin Ilimi ta Adeniran Ogunsanya tana ba da shaidar kammala karatu ta Shaidar Kammala Karatun Malunta a Najeriya wato Nigerian Certificate in Education (NCE) da shaidar kammala digiri na farko a fannin Ilimi, kasancewar tana da alaƙa da Jami'ar Jihar Ekiti.[2]
Tarihi
gyara sasheKwalejin, wacce a da ake kiranta da Kwalejin Malamai ta Jihar Legas, an kafa ta ne a shekarar 1958 a matsayin kwalejin horar da malamai ta Grade III, inda ta amshi dalibai kusan casa’in a shekararta na farko. A cikin 1982, saboda rashin isassun kayan aiki, kayan aiki na zamani da karuwar yawan jama'a, an mayar da kwalejin daga Surulere zuwa wurin da take a yanzu a Oto-Awori.[1]
Fitattun tsofaffin ɗalibai
gyara sashe- Kunle Ajayi
- Sarah Adebisi Sosan
- Oladipo Simeon Adebayo
Sassa a Kwalejin Adeniran Ogunsanya
gyara sasheA yanzu haka akwai sassa 6 a kwalejin ilimi ta Adeniran Ogunsanya, wadanda
- makarantar kimiyya
- makarantar ilimi
- makarantar fasaha da kimiyyar zamantakewa
- makarantar koyar da sana'a da fasaha
- makarantar yara da firamare
- makarantar harshe
Sanannen baiwa
gyara sasheDuba kuma
gyara sashe- Jerin makarantu a Legas
- Jerin kwalejojin ilimi a Najeriya
Manazarta
gyara sashe6°30′01″N 3°06′39″E / 6.500398°N 3.110834°E 6°30′01″N 3°06′39″E / 6.500398°N 3.110834°E