Kogin Kwa Ibo
Kogin Kwa Ibo (kuma kogin Quaibo) kogi ne da ke tasowa kusa da Umuahia a jihar Abia a Najeriya, kuma ya bi ta kudu maso gabas ta jihar Akwa Ibom zuwa Tekun Atlantika.
Kogin Kwa Ibo | |
---|---|
General information | |
Labarin ƙasa | |
Tsarin Daidaiton Labarin Kasa | 4°32′27″N 7°59′19″E / 4.5408°N 7.9886°E |
Kasa | Najeriya |
Territory | Jihar Abiya |
Hydrography (en) |
Kogin yana ciyar da wani yanki na fadamar mangrove da ke da alaƙa da raƙuman ruwa da rafuka waɗanda ke raba su da teku da ɗan ƙaramin yashi mai ƙanƙanta.[1] Ibeno, a gefen gabas na Kogin Kwa Ibo kimanin kilomita 3 kilometres (2 mi) daga bakin kogin, yana daya daga cikin manyan wuraren kamun kifi a gabar tekun Najeriya.[2]