Klousseh Agbozo (an haife shi ranar 26 ga watan Yuni 1994) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Togo wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan ɗan baya a kulob ɗin Olympique Béja da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Togo.

Klousseh Agbozo
Rayuwa
Haihuwa Lomé, 26 ga Yuni, 1994 (30 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 

Agbozo ya fara aikinsa tare da ƙungiyar Togo Dynamic Togolais, kafin ya koma Olympique Béja a ranar 1 ga watan Nuwamba 2020.[1] Ya haɗu da Béja a wasan 2-2 Tunisian Ligue Professionnelle 1 da Stade Tunisien a ranar 6 ga watan Disamba 2020.[2]

Ayyukan kasa da kasa

gyara sashe

Agbozo ya fara buga wasansa na farko tare da tawagar kasar Togo a 0-0 2020 na neman cancantar shiga gasar cin kofin kasashen Afirka da Benin a ranar 28 ga watan Yuli 2019.[3]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Agbozo Klousseh : Le Togolais débarque en Tunisie" . November 1, 2020.
  2. "Stade Tunisien vs. Olympique Béja - 6 December 2020 - Soccerway" . int.soccerway.com .
  3. Strack-Zimmermann, Benjamin. "Benin vs. Togo (0:0)" . www.national-football-teams.com .

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe