Khadidiatou Diallo, haifaffiyar ƙasar Senegal ce, ita ce ta kafa Groupe de femmes pour l'Abolition des Mutilations Sexuelles (GAMS) a Belgium.

Khadidiatou Diallo
Rayuwa
Haihuwa unknown value
ƙasa Senegal
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a gwagwarmaya

Tarihin rayuwa

gyara sashe

An yi wa Khadidiatou Diallo kaciya tun tana shekara bakwai. A shekaru 12 aka aurar ta ba tare da yardar ta ba ga wani mutum mai shekaru 33 da haihuwa.

Ta tafi Belgium a cikin 1980s. A shekara 24, ta koyi karatu da rubutu, kuma ta fara rubuta tarihin rayuwarta. Rubuce-rubucen ya kasance matattarar motsin rai don taimakawa ga shawo kan abubuwan da ta faru a baya.

Don yaki da tsatsauran ra'ayi da kaciyar mata, Khadidiatou Diallo ta kafa kungiyar Groupe de femmes pour l'Abolition des Mutilations Sexuelles (GAMS) a cikin 1966.

Manazarta

gyara sashe