Kenneth James Mumbo Thindwa (an haife shi a shekara ta 1943) masanin harhaɗa magunguna ne na ƙasar Malawi, ɗan kasuwa, kuma tsohon ɗan majalisar wakilai na Rumphi a tsakanin shekarun 2004 da 2009.[1] An haife shi a ƙauyen Chombe, Rumphi.[2] Yana da Phd a Pharmacy kuma ya yi aiki da Babban Asibitin Sarauniya Elizabeth, Sterling Winthrop (Pharmanova). Shi ne wanda ya kafa kamfanin harhaɗa magunguna Kentam Products Ltd.

Kenneth Thindwa
Member of the National Assembly of Malawi (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa 1943 (80/81 shekaru)
ƙasa Malawi
Karatu
Makaranta Jami'ar Jihar California
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da pharmacist (en) Fassara

Sana'a da ilimi gyara sashe

Ya halarci Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Mzuzu sannan ya tafi kwaleji a Jihar California ta Amurka.[2] Ya haɗu da marigayiyar matarsa, Tamara Thindwa a jami'a. Daga nan suka bar Amurka zuwa Malawi inda ya yi aiki a shagunan gwamnatin tsakiya da matarsa a bankin Reserve.[2] Ya kuma kasance a hukumar kula da harhaɗa magunguna ta Malawi, inda ya taimaka wajen kafa ka'idojin harhaɗa magunguna a Malawi. Dokta Thidwa ya zama abokin kasuwanci tare da matarsa inda suka yi haɗin gwiwa tare da ayyukan kasuwanci a Malawi, ciki har da kafa Kentam Products ltd, da Kentam Mall. Ya shiga siyasa ne ta hanyar tsayawa takara da zama ɗan majalisar wakilai na Gabas ta Rumphi.[2]

Manazarta gyara sashe

  1. "Archived copy" (PDF). Archived from the original (PDF) on 2012-02-02. Retrieved 2011-08-10.CS1 maint: archived copy as title (link)
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 "The Man behind the Shopping Centre that has Change Mzuzu". Northern Life Magazine. 1 (2): 10. n.d.