Kawata Birnin Istanbul
Kawata Birnin Istanbul birni ne mai abun ban mamaki da malaman ilmin kimiyya na kayan tarihi suka tabbata.
Kawata Birnin Istanbul |
---|
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Tarihin
gyara sasheA karnuka na 7 zuwa 11 an samu cewa daular Bizans ne ta yi mulki da al’adu da dama wanda ba ta da iyaka.
Aikin YeniKapi da aka fara wanda ya gamu da juyin juya halin CelilaiTaş wato zamanin da ake kira Zamanin Dutsi shekaru dubu 10 kenan.Ciki aikin filin Theodosius ne aka gano wasu tsaikon jikin mutane 4 da suka gabata shekaru da dama wato gabanin tarihin Miladiya 6000-6500.Wannan sintuwa da aka yi ya na da muhimmanci sosai don ya samu wuri a tarihin Istanbul don ita ce na farko da aka gano abu irin haka a kusada tsibirin birni din. A cikin tone tonen ne aka gano abubuwa ciki har da katako, da makaman tsaro.
A cewar malaman ilimin kimiyya na kayan tarihi an ta ba samun wani kauye a shekarar 8000-8.500 kuma an gano cewa mutanen kauyen sun yi cinikin dabbobi da aikin gona.Malaman sun iya sun samu cikakkun bayanai kan hakan.Wato sun gano yadda mutanen da suka yi rayuwar fatauci kamar farauta da noma inda suke sake wuraren zamansu don sauyin yanayin.
An gano wargazazzun kayayyakin yumbu wanda aka kwatanta daidai da wanda ‘yan Anadolu ke amfani da shi da kuma Çatalhöyük har ila yau.
An kuma gano kaburbura wanda suka samu shekaru dubu 8. An iya an gano yadda ake binne mamata a zamanin da wato sau da yawa wasu ana binnesu cikin kasa wasu mamatan kuma konawa ake yi masu.
A kwai al’adu da dama da ake yi wa mamaci wurin tufafin da ake sama masa, idan an konasa kuma tokar ana adanawa.Tufafin da mamatan ya sa gabannin ya mutu ana adanawa cikin dakin rataye tufafi.Wato dukkan abubuwa da kayayyakin da da aka gano ne masana suka ce an ta ba samun makabira a wurin Marmara din. Sakamakon ayyuka da masana suka yi ne aka tabbatar da tarihin birnin Istanbul tare da daular Roma, da Bizans. Shekarar da ta gabata masana sun dakatar da aikin amma bana an samu sababbin labarai game da aikin YeniKapi din.
Al’ummar Istanbul sun samu ganin kasusuwan mutane da na farko kuma sun yaba wa masanan da suka nuna himma cikin aikin.Wadannan kasusuwa masu tsawon mita 9.5 sun kai shekaru dubu takwas da dari biyar 8500.
A cikin gwaje gwajen DNA ne aka gano kasusuwan wani jinjiri mai shekaru 5 tare da. Masana din sun yi gwajen abubuwa da dama don a gano su wa ye, ciki har da gwajen akora. Wannan tone kasa da masanan kimiyya tarihi suka yi ba'a ta ba samun irin haka ba a duk fadin kasashen Turai.
Har ila yau masana kimiyya na cikin tona kasa don sun kimanta cewa za a samu abubuwa da dama wanda zai nuna yadda daular ta ke a zamanin da, kuma za a ga ice masu muhimmanci da ban sha’awa daban-daban da ke a wurin.
Tsarin kawata birnin kashi na 1 Wannan birnin ya janyo hanklan mutane da dama akan siyasa da ta gabata a cikin tsawon shekaru. Wasu mutane sun fadi. Wasu mutane kuma sun hada sojoji a kofar birnin domin su karbe iko da shi. Ko dadai tarihi ya riga ya san wadannan mutane. Toh ya sauran jama’a? Mutanen birnin da kansu? Sun iya mallaka tare da kula da birnin Istanbul ko kuma sun kasa.... Suma sun yi kokari da iko da Istanbul. Tun lokacin da aka kafa Istanbul a matsayin karamin kauye, amma a yanzu ya zama babban birni.
Sabbin al’adu da ‘yan siyasa suka kawo ga birnin Istanbul sun gauraya da tsaffin al’adu da aka sani game da birnin. Sanadiyyar hakan kuwa shi ne a cikin lokaci daban-daban mutane sun yi hijira zuwa birnin, wanda hakan ya sa aka samu al’adu daban-daban a yankin. A farkon shekarun 1960, akwai wata magana da ake anmfani da ita a kasar Turkiyya, idan ana son a gwada arzikin Istanbul; “kasar Istanbul kamar zinariya ce!”. Wannan magana ana amfani da ita ne a wurin nuna cewa idan kana Istanbul ba za ka yi rashin aiki ba kuma za ka samu tarin dukiya a wurin. Daga baya ne ake amfani da wannan magana wurin bayyana abubuwa masu kyau da mara sa kyau a Istanbul. Muma muna tunanin cewa ana amfani ne da wannan magana wurin nuna tarihi da kuma gadon manyan al’adu dake Istanbul.
Idan masu sauraronmu zaku tuna, a cikin shirinmu da ya gabata a wancan mako mun fada muku cewa, “Istanbul na da shekaru dubu 300 kuma a birnin akwai al’adu daban-daban tun tsawon shekaru 5000 a tarihi”. A cikin wannan babban birni za ka iya ganin abubuwan na al’ada a duk inda zaka tafi a cikinsa. A zamanin yau kuwa, duka inda zaka tafi a cikin birnin sai kai ta jin ihu daban-daban. Istanbul, na juyewa zuwa wani abu daban. Tun lokacin da aka zabi birnin Istanbul a matsayin babban birnin al’adu na kasashen Turai a shekarar 2010, sai jama’ar kasashen Turai suka mai da hankali zuwa wurin. Ana shirya wasan kwaikwayo, kide-kide da wake-wake, da fina-finai tare da tambayoyi game wallafe-wallafe kai da kai a birnin. Haka kuma wadannan shirye-shirye ana yin su a kasashen waje.
A kowacce shekara ana shirya wani taro mai suna “Altın Yollar” wato “hanyar zinariya” a kasar Turkiyya domin bada lambobin yabo na al’ada a tsakanin kasashen Turai. A karkashin wannan shiri ne aka shirya wasu taruka daban-daban guda hudu a birane 29 a kasashe 18 a shekarar 2010. An fara wannan shiri ne a ranar 2 ga watan Disambar shekarar 2008 inda aka tafi yawon bude ido a yankin “Karadeniz.” Wato ‘Black sea region’ a turance. Wannan taron an rubuta shi daga cikin wani littafi mai suna “”İnatcı Keraban Agha”. Bari mu karanta muku wani sashe daga cikin littafin. “Keraban Agha wani shahararren attajiri ne mai taurin kai da aka san shi daga daular Usmaniyya.
Wannan al’amari ya faru ne a rabin karni na 19 na biyu. Wata rana ya tafi cikin nahiyar Turai a Istanbul a unguwar Tophane domin ya gana da wani abokin cinikinsa wanda ya fito daga kasar Holland. Daga wurin sai suka tafi gidan Agha tare da abokin ciniki a unguwar Uskudar dake birnin Istanbul. A lokacin da zas u sai suka shiga jirgin ruwan Sarkin wurin a bakin teku. Jirgin na tsaye tsakanin hanyoyi biyu. Yan da Agha ya kalli jirgin sai abokin cinikin ya gano cewa lalle zai yi mai taurin kai. Sai Agha ya ce wa abokin ba zai biya kudin da suka yi ciniki ba zai tafi gidansa shi kadai. Domin ya yi tunanin cewa abin hawan za su yi amfani da shi zuwa gidansa zai tashi daga Tophane zuwa Kırklare, daga wurin zuwa Karadeniz, zuwa Varna, Kostence, Odessa, Soci, da kuma Batum. Daga nan kuma sai suka kara gaba zuwa Anatolia, Adapazarı, Ankara sannan ya kai Uskudar saboda jirgin ruwan Sarkin ya kulle hanya. Da ya yi tunanin zai biya kudi da yawa sai ya yanke shawarar cewa ba zai tafi gida ba. Marubuci dan kasar Faransa Jules Verne ya rubuta labarin a cikin littafinsa domin nuna yadda mutanen gabas suke. Ko da yake akwai karantar wa a cikin wannan labari amma Keriban agha ba shi da tsammani akan wata rana akwai wanda zai rubuta wannan labarin.
Altın Yollar Taron Altın Yollar. A cikin watan Afrilu da Mayu na wannan shekara, za’a ba da “izinin Evliya Celebi” domin a yi wasu taron a garuruwan Balkans. Za’a yi taron ne a kasashen Bulgaria, Macedonia, Kosovo, Serbia da Bosna-Hersek. A watannin Satumba da Oktoba na shekarar 2009 an gudanar bikin inda aka ba shi suna “izinin Piri Reis”. Nufin taron shi ne a fara zuwa Spain, da wurin zuwa Faransa, Italiya da kuma kasar Girka domin nuna al’adun yankin Karadeniz. Taro na karshe da za’a yi kuma shi ne na “Izinin Franz Liszt” an yi taron a watan Mayu 2010 inda daga tsakiyar Turai. A shekarar 2010 kuma an fara ne daga manyan biranen al’adu uku sai a kare a yankin Ruhr. Za’a fara daga Austria, Slovakia zuwa Hungary. Za’a tafi ne ana wakokin gargajiya a tafiyar. Duk tafiyar taron “Altın yolları” ce za ta hada.
Bayan tafiyar “Altın Yollar” za’a kawo karshen tafiyar ne a Istanbul inda ilimantar da mutane game da taron da aka yi. A cikin wannan taron, za’a nuna “rawa na gargajiya tare da wakokin gargajiya na Altın Yollar” da kuma “rubuce-rubucen gargajiya tare da litattafi gargajiya na Altın Yollar.” Za’a gayyaci wadanda aka yi hadin gwiwa da su wuri shirya wannan taron. A karshen taron kuma ‘Altın Yolları’ za ta yi littafi da kuma shirin gaskiya (Documentary). Mu kuma zamu ci gaba da baku labarai akan abin da ke faruwa a taron kai da kai.
Babban birni na Al’adun Turai Istanbul ya fara shirye-shiryen taron da za’a yi a shekara ta gaba. Istanbul ya fara ganawa da biranen Turai daban-daban domin gabatar da taron sabuwar shekara mai zuwa. Hukumar kungiyar sun yi hadin kai da kungiyar “İstanbul 2010 Avrupa Kültür Başkenti Ajansı” inda lokaci lokaci suke sanarwa game da wani shiri mai suna “Istanbul naka ne”. Mu kuma zamu kare wannan shirin inda muke ce muku “filin naku ne.”
Masu Sauraro mu hadu a Mako mai zuwa za mu kara tattaunawa game da tarihi, al’adu, sai mun hadu a Istanbul. Sai an jima. A madadin dukkanin abokan aiki na Muryar Turkiyya. Nine………..nake cewa mu huta lafiya.
“Idan mutum na da ikon ya kalli duniya sau daya, to wannan mutumin ya kamata ya kalli Istanbul. Akwai manyan malamai, sana’oi da yanayi mai ban sha’awa wadan nan süne suka hadu suka sanya birnin Istanbul ya zama mai muhimmaci.”
Shahararren mawakin nan dan kasar Faransa, marubuci kuma dan siyasa Alphonse Lamartine, ya yi bayani game da birnin Istanbul saboda ya zagaya daga nahiyar Asia zuwa nahiyar Turai inda ya koyi al’adu da dama a bangarorin daban-daban.
Kashi na 2 A yau yawan mutane dake rayuwa a Istanbul sun kai miliyan dubu goma sha biyu, inda girmansa ya kai kilomita dubu biyar da dari bakwai da goma sha daya har akan ce girmansa ya fi biranen kasashen Turai da dama... Bayan da aka zabi Istanbul a matsayin babban birnin al’ada na kasashen Turai a shekarar dubu biyu da goma, an yi ayyuka da taro da dama a birnin. Yau za mu ambaci wasu aikace-aikace da dama da ake yi a birnin. Bayan an kare aikin, Istanbul zai jawo hankalin mutanen duniya baki daya.
Mun bayyana a cikin shirye-shiryenmu cewa.” Istanbul ta zama babban birnin al’adun Turai a shekarar dubu biyu da goma” wannan taron zaben kungiyoyin fararen hula da kıngiyoyin gwamnati ne suka shirya. Wannan dillalai sun fara wani aiki domin sun gyara babban birnin Istanbul. Da farko kungiyoyin sun fara yara babbar cibiyar al’ada mafi muhimmanci dake Istanbul mai suna “Ataturk Kultur Merkezi”. Mun fada muku wannan ne saboda yana da muhimmmaci. Dandalin Taksim na cikin dandali mai muhimmanci da ake kalubale a birnin Istanbul. A wannan dandali na cibiyar al’adan Istanbul, ana wasan kwaikwayo, kide-kide da wake-wake kuma a wurin ne ake taron al’adu da dama.
Wannan shi yasa ofishin ministan al’adu da kungiyar dillalai da al’adu na shekara dubu biyu da goma suka dauki mataki akan cewa za su gyara wurin. An dauki matakin cewa za’a gyara wurin ne a lokacin da aka zabi Istanbul a shekarar dubu biyu da goma. Wannan gini ya kara kayayyakin al’adu da dama kuma za’a bude dakunan zane-zane a tsakiya. Wannan aikin gyara cibiyar al’adar Ataturk, babban birnin al’ada na kasashen Turai Istanbul ne ke yi. Za su gyara AKM ne daga wake-wake zuwa kide-kide, saboda ci gaba da al’adu. Za’a tsara wannan cibiyar al’adu ne domin yanda zai jawo hankalin mutane a wurin kuma za’a saka wutan lantarki saboda yanda ba za’a sami matsala ba. Saboda haka, wannan cibiyar al’ada za’a bude kwana dari uku da sittin da biyar dare da rana.
Kamar yanda muka ambata da farko, za’a saka wutar lantarki, tsaro, wurin gyara sauti da wasu abubuwa da dama. Wannan wuri an gina shi a shekaru da dama da suka wuce kuma ba a samu wanda zai gyara ba, shi yasa wannan kungiyar al’adu suka dauki mataki akan cewa za su gyara.
Kayayyakin ado da kasashen China da Japan suke amfani da shi suke jawo hankalin mutanen duniya sun yi koyi daga fadar Topkapı dake babban birnin Istanbul. An gina fadar Topkapı ne a shekarar dubu daya da dari hudu da saba’in da takwas bayan Fatih Sultan Mehmet ya jagoranci yakin karbr Istanbuli, bayan shekara dari uku da tamanin sai aka kuma gina fadar Dolmabahce a karkashin jagorancin Sultan Abdulmajid inda aka mai da wurare biyun a matsayin majalisar daular Usmaniyya.
Fadar Topkapı da Dolmabahce su ne fada biyu da har yanzu ake gyaran ciki tun lokacin daular Usmaniyya da ake gyarawa lokaci zuwa lokaci. Shahararren abu daga cikin fadar shi ne dakin girki. Shahararren mai gini Mimar Sinan ne ya gina wannan dakin girki; wurin yana daukan masu yin abinci guda dubu daya da dari biyu da kullum suke girki kuma a yau idan ka je kasashen China da Japan, zaka samu irin abincin da suke yi a lokacin. A lokacin kayayyakin abinci dubu goma sha biyu ne suke amfani da shi, amma a yau sauran dubu biyu da dari biyar.
Idan ka duba yanayin lokacin, zaka ga cewa abinda Sultan ke tsoro shi ne a saka guba a cikin abinci domin a kashe wani. Saboda Sultan na tsoron wannan abu ne yasa kowani lokaci sai an wanke kwanon abinci sa’annan su fara cin abincin.
Domin a samu a nuna wadannnan kayayyakin abincin fadar China da Japan a fadar Topkapı ne kungiyar al’adan babban kasashen Turai na shekarar dubu biyu da goma ne suke gyara fadar. Bayan an gama gyara wannan fadar mutanen Istanbul da duniya baki daya za kaga kayar al’adu da dama a wurin. Ta haka ne mutane za su gane asalin kayan al’adun babban birnin al’adun Istanbul. Dukkan wadanna aiki ana yi domin kare kayayyakin al’adun wurin.
Ba wurin tarihi guda biyun kadai za’a gyara a garin ba. A cikin aikin kungiyar babban birnin al’adun Istanbul, za’a gyara ofishin shugaban kungiyar inda za’a sake gyaran wuraren tarihi guda tamanin da takwas. A cikin wannan wurare, akwai masallacin Sulaimaniyya wanda aka gina a cikin shekaru dari hudu da suka gabata. Sa’an nan, za’a gyara masallatai kamar, Nuruosmaniye mai taga 171, masallacin Valide Sultan, masallacin Fatih, da kuma masallacin Yavuz Sultan Salim. Za’a yi gyare-gyarensu. Za’a kuma gyara kasuwar Masar dake Istanbul.
A yanzu ana shirye-shiryen gyara wuraren tarihin. A wani mako za mu ci gaba da baku labarin shirin gyare-gyaren wuraren tarihi. idan an kammala gyare-gyaren wuraren tarihin, birnin Istanbul zai zama inda ke dauke da wurin tarihi da yafi ko’ina a duniya baki daya.
Kashi na 3 Akwai ayyukan da ke ci gaba da shi a yanzu wadanda aka fara a shekarun baya a birnin. Wadanan ayyukan kungiyar babban birnin al’adun Turai ce ke ci gaba da yinsu. Kasar wannan birni kamar kasar baitulmali ce. Mun taba fada muku cewa duwatsun kasar Istanbul kamar zinari amma ba duwatsun kadai ba ne. Saboda tekun sa birnin ma zinariya ce...
Akwai wasu ayyuka da ak na tsawon wani lokaci a tekun. Wanan aiki shi ne mafi muhimmancin da aka yi a tekun, wannan aiki mai suna Marmaray shine wanda zai hada dukkan duniya a karkashin teku.
Tun daga shekarar dubu daya da dari takwas da sitin ne aka bayyana ra’ayin cewa ana son a yi hanyar jirgin kasa a karkashin teku. Sai wannan ra’ayi a wannan shekara kamar mafarki ne saboda fasahar lokacin ba ta kai a yi aikin ba. A shekarar 1902 sai aka fara zane-zane game da aikin. Amma da yake babu isashen kayan aikin hanyar jirgin, sai aka tsayar da aikin. Sai aka kuma tayar da aikin a shekarar dubu daya da dari tara da tamanin. A karshen shekarar dubu daya da dari tara da tamanin da bakwai, sai kasar Turkiyya ta dauki mataki na farko game da wannan aikin Marmaray. An tattauna game da wannan aiki a cikin shekaru da dama. A watan Agusta na shekarar dubu biyu da hudu sai aka fara ainihin aikin.
Idan aka gama aikin, zai zama cewa an gama yankuna biyu da tekun ya raba a karkashin ruwa. Ta haka ne zai zama cewa hanyar jirgin kasa da aka yi a karkashin ruwan ne ya hada yankuna biyun.
Wani abin mamaki game da wannan aikin shi ne musamman ilmin kimiya na kayan tarihi dake ciki. Har zuwa yau ana ci gaba da tono rami karkashin ruwan domin yin hanyar. Canje-canje da aka sanya na ci gaba wurin aikin, an samo shi ne ga masu karatun ilmin kimiya na kayan tarihi. Daya tashar hanyar jirgin sama da za’a yi a karkashin ruwa zai kasance a Yenikapı na yankin Turai. Saboda haka an fara aikin gine-gine da tonon rami a wurin. Sai dai, wannan zai zama karo na farko da wannan yankin Istanbul za ta samu da Katanga. Abin mamakin game da katangar bai kare ba. Katangar zata kewaye tashar jirgin ruwan Theodosius. Lokacin da aka fara gina tashar Marmaray a Yenikapı sai ba san abinda ke karkashin kasar ba. Da aka toni rami nisan mita 8 sai aka ci karo da wani jirgin ruwa wanda aka yi da katako a karkashin kasar. Da aka ci gaba da tono ramin kadan sai aka kuma samu jirgin ruwa na biyu a karkashin ruwan. Wannan shi ne halin da ya sa aka fara tono ramin tashar Yenikapı da wuri. Tonan ramin tashar da aka yi a Yenikapı a shekara dubu biyu da hudu, shi ne babban ramin da aka tone domin gina hanyar kasa a karkashin ruwa a tarihin Turkiyya. Kuma ya taka rawa mai muhimmacin wurin haskaka tarihin Istanbul. Yanzu haka, aikin da ake yi a Yenikapı na cikin babban aikin ilmin kimiya na kayan tarihi na ban sha’awa a duniya. wannan aiki yana haskaka tarihin birnin na shekaru dubu goma. Aikin wannan sashe da ake kiransa da tashar jirgin ruwan Theodosius, fiye da wurare daban-daban masu girma guda talatin ne aka gwada. Wannan wuraren da aka gwada, ya rubuta littafi a kansa mai suna “Tsohon Jiragen Yenikapı.”
A yau an san cewa, tashar jirgin ruwa dake tudu mai nisan mita dari biyar a lokacin Roman-Byzantine tashar jirgin ruwan Istanbul ce, bayan hatsi daga Masar a karni na bakwai, sai muhimmacin tashar jirgin ruwan ya ragu, daga wannan lokaci sai aka fara anfani da shi dalilan sojoji. Sai dai wannan lokaci ba san sai daidai inda ya ke ba. Saboda tashar da jiragen ruwan, sun saura karkarshin yashi a lokacin da kogin Lycus ya ci tudun. A cewa da aka samu daga wani misali, ana tunanin cewa kogin ya ci tudun ne a lokacin da tsunami ta buga tudun bayan girgizar kasa ta faru a wurin. A wannan yanki a lokacin daular Uthmaniyya an yi amfani dashi wurin horar da Lambu kuma lokacin daga wurin ake ba ‘yan Istanbul da kayan lambu. Lokacin da ake tone ramin an samu kayayyakin tarihin tsakanin karni bakwai zuwa karni goma sha daya,dari hudu da hamsin daga cikinsu kayayyakin al’adu ne kamar kayan masu tukin jirgin ruwa, igiyoyi da kuma anka. Bugu da kari, an gano wani hanyar da mahaifiyar Sarkin sarkunan Constantine ta bi a kan teku wanda mutane basu sani ba a lokacin da kuma hayar da matafiya suke bi a lokacin daular Uthmaniyya.
Sunken jiragen ruwa, an yi su ne a karni na tara da goma sha daya wanda aka fi sani da shekara duhu, kuma a wannan lokacin an yi jiragen ruwan yanda zai haskaka hanya. Saboda yadda kasa yake a lokacin ko da an tsare su da kyau bai zai iyu ba domin haka sai suka yi ma jiragen ruwan shiri na musamman. Saboda haka, kullum sai su rike wani abu kamar laima domin kiyaye su daga haske da kuma zafin rana. Farkon jiragen ruwan na kaiwa inda yanzu ake tone ramin Yenikapı kusa da Jami’ar Istanbul domin tsaro.
Kafin a dauki kayayyakin da aka samu a karkarshin kasar, ko wane daya daga cikin kayan an daukin hotonsa, bayan haka aka basu lamba sa’anan a saka a cikin kwamfuta. Wasu daga cikin kayayyakin an kai su Jami’ar Istanbul inda aka kafa dakin gwaje-gwaje na farko da aka kafa domin sake maimaitasu. A nan akwai kayayyakin aiki wanda za’a iya sake maimaitasu. Ana kuma anfani da sunadarai domin gyara su saboda zafi da ya kamasu lokacin da suke karkashin kasa.
Kayan da aka samu a wannan yankin, daraktan kula da kawata birnin Istanbul tare da kungiyar babban birnin Al’adun Turai na shekarar dubu biyu da goma ne suka hada kansu. Wannan kungiyar, su suka fara aikin gina tashar jirgin kasa a karkashin ruwa wanda zai zama daga cikin mayan aiki a duniya. Ana ci gaba da shirye-shirye a kan aikin. Bisa ga wannan aikin yankin Yenikapi, kayayyakin da aka samu a yayin tone ramin, sabon hanyar jirgin ruwa, jiragen ruwa, za ajiye a gidan kayan gargajiya domin nunawa mutane. Za’a rufe saman kan kayan ne da karfe da kuma gilashi. Gidan kayan gargaiyar za’a bude wa mutane masu tafiye-tafiye domin tunatar dasu tarihi.
Bayan an gama aikin hanyar jirgin kasa a karkashin ruwan wato Marmaray, Yenikapı zai sha wata babbar canji. Bayar da kwazo wurin wannan aikin yana sa mutane farin ciki kuma yana haskaka Istanbul. Hakika, wannan aiki zai faranta wa al’umma rai. Sabon mako za mu baku labarin gefen Istanbul mai ban sha’awa, sai anjima.
Kashi na 4 Barkan mu da saduwa a shirin mu da babban birnin al’adu Istanbul. A yau zamu baku labari tarihin shaharerren wurin da mutane da ke zuwa kafin su bar birnin Istanbul. Zamu baku labarin wanda ke dauke da shekaru dubu dari da dari biyar a cikin tarihin zane-zane da kuma wanda sunansa ke cikin jerin aikin gyare-gyare da aka yi a shekarar dubu biyu da goma wato Ayasofya.
Ayasofya shahararren dandalin Sultan ahmet ne, inda akwai kayayyakin tarihi mai yawa. Idan ka ziyarci ko ka zagaya a dandalin ba zai yi wuya ace ba ka ga Ayasofya ba. Amma cikin ginin ya fi wajensa ban sha’awa; saboda kamar fada ne da kyawunta ke kama ido. Saboda haka, maimakon mutum ya tsaya a waje ya kalli Ayasofya to gwara ya shiga ya kalli cikinta. Wannan gini da ake cewa shi ne babban gini na 8 a duniya, Yau shi ne babban coci na hudu a duniya. Wannan coci an mai da shi masallaci a lokacin daular Usmaniyya; a shekarar dubu daya da dari tara da talatin da shida kuma sai Ataturk kuma ya mai da shi gidan kayan gargajiya.
Wasu masana tarihi sun ce farkon Ayasofya an gina shi ne a shekarar dari uku da ashirin da hudu lokacin sarkin sarakuna Constantine na I. A lokacin da aka yi an yi masa ginin Basilika katako ne aka rufe, bayan rikicin da wasu ‘yan tawaye suka yi sai ya kone. Bayan haka sai sarkin sarakuna Theodosius na II ya gina Ayasofya karo na biyu a shekarar dari hudu da goma sha biyar a matsayin gidan ibada. Wanan karo kuma ginin Basilika aka yi masa inda kuma sarkin sarakunan Justinyen wanda aka fi saninsa da suna “Nika” kuma suka yi sabon rikicin suka kona Ayasofya. Bayan wannan rikici da aka yi, sai sarkin sarakuna ya yanke shawarar cewa zai gina babban coci wanda ba taba gina irinsa ba, ta haka ne sai ya kira shahararrun masu gini kamar Miletos İsidoros tare da dan Tralles Anthemios suka zo suka gina Ayasofyan wacca ake gani a yau. An fara ginin ne a filin da aka gina basilika a shekarar dari biyar da talatin da biyu, inda aka yi anfani da wasu ginshikai daga Anatolia, an yi da duwatsu masu launuka daban-daban wurin ginin; A karkashin marinjaya dari, an yi anfani da ma’aikata guda dubu goma wurin ginin wanda ya dauki shekaru biyar, a shekarar dari biyar da talatin da bakwai sai aka yi bikin bude cocin. Ayasofya ne tsoho kuma mafi saurin babban cocin da aka gina a duniya. Sunanshi na musamma Hagia Sofia ne. Wani mai ginin Roman ne ya gina kubbar cocin. A wannan lokaci, ana anfani ne da wani abu madauri wurin gina kubba. Duk da haka, a tarihin gine-gine wannan shi ne karo na farko da aka yi da wani abu mai kusuwahu wurin gina kubba.
An gina Ayasofya ne domin nuna takama da yarda. Daga baya ne aka mayarda wurin a matsayin wurin bada labarai da nuna alama. Kowa ya yarda cewa irin wannan wuri sai dai da taimakon Ubangiji ne aka iya aka gina. Ko da yake an gina Ayasofya a karni na shida a lokacin Byzantine, kuma baya ga shi ba a taba da samun irin wannan gini ba, kuma har zuwa yau ba a taba samun gini mai kubba ya sayar har shekaru dari tara ba. Duk da haka a shekarar dari biyar da hamsin da takwas, an yi wata girgizar kasa inda ta hallaka kubban. Kubba da aka yi ta biyu ya fi girma amma sai dai kanana ne. Wannan kubba kuma aka fara a cikin sabon karni, an kusa gina rabinsa sai ya rushe har sau biyu. A sherar dubu daya da dari hudu da hamsin da uku da Sarkin musulman daular Uthmaniyya Fatih Sultan Mehmet ya yi nasarar mamaye garin, sai ya ceci Ayasofya inda ya mayar da ita masallaci. A karni na goma sha shida, sai aka sake alkuki da kuma rubuce-rubecen cikin ginin ta hanyar musulunci. A tsakiyar karnin goma sha tara kuma, sai mai gine-gine Fossati suka fara gyare-gyaren gini tun daga shekarar dubu daya da dari casa’in da talatin har suka kawo halin da yau muke ganin Ayasofya.
A tarihin Byzantine, Ayasofya na da muhimmaci sosai. Saboda dukkan bikin sa wa sarakuna kambi da bikin nasara duka a wurin ake yi. Da yawa daga cikin wadannan zane-zane an yi su ne bayan zamanin 'iconoclasm' wato zamanin da aka dinga rushe mutum-mutumi da lalata zane-zane saboda dalilai na addini ko na siyasa. A daya cikin shirin ma an yi wani sassaka dake tsaye tsakanin sarukuna biyu; Constantine da Justinian, a kusa da shi kuma aka ajiye Nana Mariam da Yesu akan cinyanta, a gefe kuma sai aka yi rubutu dake nuna ruwan Istanbul na zuba a Ayasofya. Saboda haka masu ziyarar wannan bangare suna ganin kyawon wurin. A nan, kowa ya shiga wannan bangare yana mamakin wurin. Saboda idan ka shiga wurin sai ka ga kamar kubban cikin iska ya ke kuma ka kasa mai da hankali akan ginin baki daya. An yi rubuce-rubuce aka bako da kuma bisa ginin da launi daban-daban. An yi anfani da launi daban-daban guda uku aka yi rubuce-rubuce daban-daban uku akan kowacce kubba. A cikin ginin kuma akwai wurin da matan sarukana ke taruwa da kuma inda ake taron coci.
Musulmai sun dauki Ayasofya a matsayin wurin bauta mai tsabta. An kewaye ginin mihrab da zane-zanen Turkawa da Sin masu kyau. Daga cikinsu akwai rubutun wani shahararren marubucin Turkiya mai girma Kazasker Mustafa Izzet inda ya rubuta ayar Alkur’ani mai girma akan daya daga cikin kubbobin. A Ayasofya, akwai kaburburan manyan daular Usmaniyya da dama, da makarantu, da kuma misalin dakunan karatu da Turkawa ke anfani da shi a yau. Kaburburan; ciki da zane zanen wajen shi kuma an yi rubuce-rubucen daular Usmaniyya akai. abinda muka baku labari kadan kenan daga cikin fitacciyar tarihin Ayasofya. Saboda gaskiya ba za a iya baka cikakkiyar labarin kyawun Ayasofya ba domin sai ka gani da kanka.
Masallacin Ayasofya na cikin jerin kayan tarihin hukumar kulawa da ilimin kimiyya da raya al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) masu muhimmanci, wannan shi ne ya sa a shekara ta dubu daya da dari tara da casa’in da biyu zuwa shekarar dubu daya da dari tara da casa’in da uku UNESCO suka bayar da taimako wurin gyare-gyarensa. Wannan shine dalilin da yasa kubban da aka yi mai tsawon mita ashirin da shida ko ashirin, aka mai dashi zuwa tsawon mita hamsin da biyar tare da nauyin karafe dari da tamanin da daya. Wannan karafen da aka yi anfani dasu, ya gyara kubban da aka yi a shekaru goma sha shida da suka gabata. Amma a shekarar dubu biyu da goma, an kai wannan gidan tara kayan tarihi. Saboda ofishin ministan al’adu da kungiyar dillalan raya al’adu na shekarar dubu biyu da goma suka dauki mataki akan cewa za su gyara Ayasofya. A taron da kungiyar dilalan suka yi a ranar goma sha bakwai ga watan Janairu, sun yi bayanai game da gyare-gyaren da za su yi a wurin. Har ma sun sanarda cewa sun fara shirye-shirye. A karshen watan Yuni na wannan shekara, za’a kammala shirye-shiryen gyaran wurin. A halin yanzu, za’a fara gyaren da aka jima shekara da shekaru a na jira. A cikin gyare-gyaren, za gyara dakin karatun Mahmut na I kuma za’a gyara kaburburan dake wurin; tare da lambun wurin da kuma dakin ajiye kayan al’adu. Ana sa ran cewa kafin karshen watan Nuwamba an kammala gyare-gyaren Ayasofya.
A shekarar dubu biyu da goma, babban birnin al’adu kasashen Turai zai zama babban wuri da miliyoyin mutane za su ziyarci, kuma za su sa a ganin Ayasofya bayan an kammala gyare-gyaren wurin.
Kashi na 5 Shin kun taba tunani abin da ke sa birni ya yi kyau? Shin tarihinsa ne, ko yanayin garin ne, ko kuma yadda al’adun garin suke ne? Idan birnin Istanbul ne; to ruhin garin ne mafin muhimmancin abinda ke gyara garin. Garin na da ban mamaki amma kuma yana cike da farin ciki! Ko’ina ka je a cikin garin, za ka samu farin ciki. Idan ka shiga garin, sai ka ga kamar baka son ka fita daga cikinsa. Idan farin ciki kake nema, to sai a Istanbul.... Wannan gari ne dake sa mutane farin ciki tun a zamanin da.
Istanbul gari ne dake dauke da mutanen kasashe daban-daban, da addinai daban-daban, saboda a garin akwai mutanen Roman, Byzantine, da kuma daular Uthmaniya inda kuma akwai mabiya addinai kamar Kirista, Yahudawa, da kuma Musulmai.
A Istanbul, masu sana’a da dama daga ko’ina a duniya sun zabi su je birnin domin su yi rayuwa; ba don yana Turai ko nahiyar Asiya ba, ba don yana Gabas ko Yamma ba, ba don sabuntarsa ko tsufansa ba, ba don al’adunsa, saboda dukkan wannan yana cikin wannan birnin, wannan shi ne ya sa kungiyar babban birnin al’adu na nahiyar Turai ke daraja shi.
Yadda masalolin tattalin arzikin da kuma zamantakewa tare da fadan kabilanci da kuma tashin hankali na addini ke kara girma a duniya; birnin Istanbul ne misali mai kyau da za a bayar wurin yadda za kawo karshen wadannan matsaloli. Saboda siffofi da wannan gari ke da shi a nahiyar Turai suka ce ya da ce a zabe shi a matsayin babban birnin al’adu na nahiyar Turai saboda sake gwada wa duniya irin muhimmanci da birnin ke dauke da shi. Ko da dai cewa duniya sun san cewa Istanbul, birni ne dake cike da al’adu. Bayan aikace-aikace da kungiyar birnin al’adun na Istanbul shekarar dubu biyu da goma suka yi, sai birnin ya zama cibiyar al’adu da kuma sana’a. Wadannan aikace-aikace da ake yi na matukar farantawa mutane.
An kafa kungiyar babban birnin al’adu na nahiyar Turai akan “abubuwa guda hudu”, abubuwan da aka kafa a kansu sune; yanayin iska, ruwa, ƙasa da wuta. Idan za mu iya tunawa; kafin ilimin bunkasar tattalin arzikin kasashen duniya ya bayyana a ko’ina, a yammancin duniya Kristoci na da nasu irin tunani kuma musulmai dake gabashin duniya kuma na da nasu irin tunanin, amma sai dai tunanen da suke yi duka akan abubuwa hudu ne. tunanni akan abubuwa hudun shi ne, yanayin iska, ruwa, ƙasa da wuta kuma kowanne abu a doron kasa yana dogara a kansu. Asalin wannan tunani da aka dogara akai, an samo shi ne a yammacin Anatolia. Saboda haka kafin a zabi Istanbul a matsayin babban birnin al’adun Turai, sai da aka yi magana akan wannan tunanin da ake da shi. kungiyar babban birnin al’adu na nahiyar Turai sun fara ayyukansu ne akan wadannan abubuwa guda hudu. Farkon aikin su ne “Jigon Kasa” wanda aka fara a ranar daya ga watan Fabrairu. Dama mun riga mun fada muku cewa wannan aikin zai dauki tsawon wata uku. Shin za ku iya tunawa da abinda muka fada muku? Ayyukan su ne dandalin Ataturk, tashar jiragen ruwan Theodosıus.
Aikin da Hukumar Raya Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) ke yi Wannan aikin ta hukumar UNESCO, ginin cibiyar al’adu da aka kammala ginawa a ranar daya ga watan Fabrairu a shekarar dubu biyu da tara inda a yau take taimakawa wasu ayyuka guda uku da ake yi a birnin Istanbul. Wa’anan ayyuka sune, Sassan yakin Eminonu, da ayyukan Sirkeci tare da wani aiki mai suna ‘Masterplan Istanbul. Wadannan ayyukan kuma za su shiga cikin jerin sunayen Hukumar Raya Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya. Misali, a cikin wannan aikin, UNESCO za ta gabatar da katangun Istanbul kuma za ta kiyaye ta. Za’a kuma gyara Eminonu da kuma karakoy.
Yeditepe wani shahararren wuri ne a birnin Istanbul. A wurare da yawa ma ana kiran birnin Istanbul da suna Yeditepe. Wannan Yeditepe shi ne a yau aka raba biyu ake kiransu da suna Eminonu da Fatih har wasu ma na kiransa da wurin tarihi. Yeditepe wuri ne dake dauke da cikakken tarihi kuma a daular Uthmaniya wurin ne aka yi mulki ba tare da wani fada ba. Saboda Byzantine sun yi rayuwa a garin a zamanin daular Uthmaniya ba tare da wani tashin hankali ba. A garin Istanbul akwai; majami’u, makarantun addini, wurin rubuce-rubuce, fadar da kuma wasu abubuwa iri iri. A nan ne, aka yi rubuce-rubuce a cikin harsuna da dama game da addinai da kuma al’adu. Saboda wurin nada muhimmanci ne yasa za yi gyare-gyare. A takaice de, za’a yi gyare-gyaren da zai daraja Yeditepe na birnin Istanbul.
Cibiyar al’adun Hasan pasha na daya daga cikin wurin da kungiyar babban birnin al’adu na nahiyar Turai za su gyara. Ginin Hasanpasha ne da masu gine-ginen kasashen Faransa da Jamus suka gina a shekarar alif dari takwas da tamanin da bakwai. An yi wannan gini ne domin ya haskaka sauran gine-ginen birnin Istabul. Ginin Hasanpasha na ciki tsofoffin gini dake da yankin Anatolia. An yi wanan gini ne akan fadin filin ekoki talatin da biyu inda ake samar da iskar gas a wurin. A shekarar alif dari tara tisi’in da tara kuma sai aka kawo karshe aikin samar da iskar gas din. Kungiyoyi da dama sun yi kokarin barin wannan wurin ya zama gidan ajiye kayayyakin tarihi amma sai dai ya gagara. Har ma yana can hankalin mutanen dake rayuwa kusa da wurin. Amma a yanzu burin kungiyar babban birnin al’adu na nahiyar Turai shine su gyara wurin. Da farko za yi anfani da aikin da gwamnan birnin Istanbul ya shirya ne wurin gyara gidan. Daya daga cikin abubuwa masu muhimmanci game da al’amarin aikin shine, hukumar kungiyar babban birnin al’adu na nahiyar Turai sun riga sun san yadda za aiwatar da aikin. İdan aka kare gyare-gyaren ginin Hasanpasha, to wurin zai zama daya daga cikin wurare masu muhimmanci a birnin Istanbul.
Kashi na 6 Ana ci gaba da gyare-gyaren babban birnin al’du na nahiyar Turai. “Sur-i Sultani Stratejik Vizyonu” wato “Suri Sultan Strategic Vision” a turance ne sunan gyare-gyaren da ake yi. Fadar Sur-i Sultani Topkapı, wuri ne dake da matukar kyau, saboda a cikin fadar akwai wani babban filin furanni da ake kiransa da suna “Gulhane Park”. Wannan fadar, kusan kowanne mai yawon bude ido da ya zo Turkiya yakan ziyarci wurin kuma ana ba shi labarin wurin. Hakika fadar na cikin cibiyar tarihin garin.
A yau, fadar Topkapı na cikin gidan adana kayan tarihi mai muhimmanci wanda aka bude a zamanin Sultan Abdul Majid a karni da goma sha tara. A wannan lokaci, Idan jakadan Turkiya suka ziyarci fadar Topkapı, sai a nuna musu dukiyoyin dake cikin fadar. Bayan haka ne sai nunawa mutane dukiyoyin dake cikin fadar ya zama kamar al’ada. Wannan fadar, Fatih Sultan Mehmed ne ya bude ta shekarar alif dari hudu da saba’in da takwas inda akalla shekaru dari tamanin kenan tun daga zamanin daular Uthmaniyya. Fadin fadar akalla mita dubu dari bakwai. A cikin wannan fadar, akwai wurare kamar wurin shirya liyafa, fadar gwamnati, da wani wurin da mutanen birnin ke taruwa, masallatai, dakin karatu da kuma dakin girki. An sa ma wannan fadar suna Topkapı ne saboda tana gabar teku kuma a kowanne lokaci mutane na taruwa a gabanta.
Da farko furanni na Gulhane Parkı na wajen fadar ne. A wajen za ka furanni da dama, wannan ne ya sa wasu mutane ke kiran fadar da suna filin furanni. Girmanta ya kai kadada dari da sittin da uku, kuma a shekarar alif dari tara da goma sha biyu sai aka bude wa mutanen domin kowa ya iya zuwa ya kalla. Gulhane Parkı, wuri ne mai ban sha’awa saboda haka ne mutane da dama a birnin Istanbul suke zuwa wurin da zuri’arsu domin shakatawa. A wurin, ana yin wasanni kamar wasan tseren doki da dambe da kuma wasu wasanni. Babu shakka wannan wuri na dauke da tarihi mai muhimmanci. A zamanin Daular Uthmaniyya, a nan ne Sultan Abdul Majid tare da wasu mutane suka taru suka tattauna yadda za a kiyaye rayukan mutane, dukiyarsu, mutuncinsu tare da tattalin arzikin kasar. A shekarar alif dari takwas da tamanin kuma, farkon abinda AbdulHamid na biyu ya bukata a yi shi ne a mayar da Gulhane Parkı a matsayin gidan ajiye kayan al’adu ta haka ne sai shaharraren mai zane-zane da gine-gine mai suna Osman Hamdi Bey ya mayar da wurin kamar yadda aka bukata. A wurin ne aka ajiye manyan rubuce-rubucen daular Uthmaniya. A nan aka amince da harufan boko da shugaban kasar a lokacin jamhuriya Ataturk ya bar aka rubuta a shekarar alif dari tara da ashirin da takwas; a wannan lokaci, an rubuta harufan ne akan bakin allo. A yau, idan kaje Gulhane Parkı za a ga yadda aka mayar da shi kamar dandali inda ake yin nishadi da wasu taruka daban-daban a birnin Istanbul.
A zamanin daular Bizans, katangar da ta zagaye fadar Topkap da filin Gulhane, kuma ta hade su da gabar tekun Marmara na da tsawon mita dubu da dari hudu. Fadar Topkapı, an bude ta ne a shekarar alif dari hudu da saba’in da takwas a bisa umarnin Fatih Sultan Mehmet. A fadar Topkapı, an gina katanga kusan ashirin da biyar ko ashirin da takwas domin a kare ginin. A jikin bangon da aka gina, akwai manyan kofofi kamar Otluk da Haliç sa’anan akwai kanan kofofi guda biyar wanda suka hade da Ayasofya.
A takaice dai, abinda muke kokarin baku labari shi ne irin aikace-aikacen da kungiyar dillalan raya al’adu na shekarar dubu biyu da goma suka yi wa Sur-i Sultani da gidajen tarihin dake kusa da ita. A cikin ‘yan shekarun nan, an yi wasu aiyuka a wurin domin gyara wadannan wurare. Amma wannan karon, kungiyar dillalan raya al’adu na shekarar dubu biyu da goma sun dauki nauyin gyara wurin ne baki daya. Don haka, an fara gyare-gyaren wurare kamar, gidan ajiye kayan al’ada na fadar Topkapı, gidan wallafe-wallafen tsofoffin waka, gidan mutanen Sin, filin fadar Topkapı da kuma da Ayasofya, da majami’a dake nan a lokacin Byzantine mai suna Irin, tare da dukkan gidajen yi kuda aka kafa a lokacin daular Uthmaniya mai suna “Darphane-i Amire”. A cikin aikace-aikacen da za yi, za a sake gyaran katangun Darphane-i Amire; bayan haka za a sake gyare-gyaren sauran gidajen daular baki daya. A cikin aikace-aikacen kuma, za gyara Gulhane Parkı domin kiyaye cikakken tarihi dake tatare a wurin. Manufofin gyara Sur-i Sultani su ne, a nuna wa mutane abubuwan dake ciki; Ba tare da kuma an samu kowacce irin matsala wurin ziyarar wurin ba.
An bayyana cewa, wadannan wurare da za a gyara dukka na cikin jerin kayan tarihin hukumar kula da Ilimi, kimiyya da raya al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO). Kamfanonin daka tallafawa wanan aiki su ne, kamfanin da suka gyara gidan ajiye kayan al’adu na Victoria and Albert dake birnin London, da kuma Guggenheim dake birnin Bilbao, da Ashmolean na birnin Oxford, da na kasar Misira dake birnin Alkahira tare da wasu manyan gidan ajiye kayan al’adu a duniya.
Darajar Sur-i sultani da kuma fada, da wurin shakawata da kuma wurin tunawa na ci gaba da karuwa a kowani shekara. Saboda lalle ne darajar wurare masu cikakken tarihi na ci gaba da karuwa. Amma idan wurin bai da cikakken tarihi, to babu shakka mutane da dama ba za su ga darajar wurin ba. Saboda ta hanyar kiyaye wurin ne za iya nuna wa sauran mutanen da za su zo daga baya. Ta haka ne babban birnin al’adu na Istanbul ke ci gaba da kyau.