Karim Attoumani (an haife shi ranar 24 ga watan Maris 2001) ƙwararren ɗan ƙwallon ƙafa ne wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron baya ga kulob ɗin Dijon B. An haife shi a Faransa, yana buga wa tawagar kasar Comoros wasa.[1]

Karim Attoumani
Rayuwa
Haihuwa Saint-Denis (en) Fassara, 24 ga Maris, 2001 (23 shekaru)
ƙasa Faransa
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 

Sana'a/Aiki

gyara sashe

Attoumani ya fara buga wasan ƙwallon ƙafa yana ɗan shekara 13 bisa ga umarnin mahaifinsa, kuma samfurin matasa ne na kwalejojin kulab ɗin Réunionnais AG JS Deux-Rives, Parfin, JS Champ-Bornoise, OCSA Léopards, kafin ya koma ƙasar Faransa tare da Montpellier a cikin shekarar 2019. [2] A ranar 23 ga watan Satumba 2021, ya koma reserves ɗin kungiyar Dijon.[3]

Ayyukan kasa da kasa

gyara sashe

An haife shi a Réunion, Faransa, Attoumani asalin Comorian ne. Ya wakilci Comoros U20 a 2022 Maurice Revello Tournament. An kira shi zuwa babban tawagar kasar Comoros don tsarin sada zumunci a watan Satumba 2022.[4][5] Ya buga wasansa na farko da Comoros 1-0 a wasan sada zumunci da Tunisia a ranar 22 ga watan Satumba 2022.[6]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Karim Attoumani" .
  2. "Football : Karim Attoumani rejoint le centre de formation de Montpellier" . Réunion la 1ère .
  3. "Karim Attoumani va rejoindre Dijon" . September 23, 2021.
  4. Houssamdine, Boina (May 28, 2022). "La liste finale des Comores pour le Tournoi Maurice Revello 2022" .
  5. Lantheaume, Romain (September 16, 2022). "Comores : deux nouveaux de l'OM dans la liste pour la Tunisie et le Burkina Faso" . Afrik-Foot .
  6. Houssamdine, Boina (September 22, 2022). "Les Comores s'inclinent en amical contre la Tunisie" .