Kanta Museum
Kanta Museum Wani gidan kayan gargajiya ne a Argungu, Najeriya, kusa da babbar kasuwa. An gina ginin a shekarar 1831, an sa wa ginin sunan Muhammed Kanta, wanda ya kafa Masarautar Kebbi a shekarar 1515. Yakubu Nabame, tsohon Sarkin Kebbi ne ya gina shi, kuma ya kasance fadar sarki har zuwa 1942 lokacin da turawan Ingila suka gina sabuwar fadar mulki a zamanin Muhammad Sani . Bayan ginin ya zama babu kowa, a ranar 1 ga Yuli, 1958, ya buɗe a matsayin gidan tarihi, yana ba da haske game da rikice-rikicen tarihin jihar Kebbi . Gidan kayan tarihi ya kasu kashi goma sha daya kuma yana da tarin makamai masu ban mamaki, wadanda suka hada da laya, mashi, takuba, itace, duwatsu, baka da kibau, bindigogin gida har ma da ganguna da ake nunawa.[1]
Kanta Museum | |
---|---|
Hukumar Kula da Gidajen Tarihi ta Kasa ethnographic museum | |
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya |
Jihohin Najeriya | Jahar Kebbi |
Ƙananan hukumumin a Nijeriya | Argungu |
Coordinates | 12°44′58″N 4°32′12″E / 12.7495°N 4.5367°E |
History and use | |
Opening | 1958 |
Manager (en) | Hukumar Kula da Gidajen Tarihi ta Kasa |
Contact | |
Address | PGXP+QMF, 861101, Argungu da Kanta Museum, P.M.B. 1001 Argungu, Kebbi State. |
Offical website | |
|
Manazarta
gyara sashe- ↑ Next Archived 2011-07-21 at the Wayback Machine