Kagendo Murungi
Rayuwa
Haihuwa 7 Disamba 1971
ƙasa Kenya
Mutuwa Harlem (mul) Fassara, 27 Disamba 2017
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a Mai kare hakkin mata, mai tsara fim da darakta
IMDb nm4321849

Kagendo Murungi (7 Disamba 1971 - 27 Disamba 2017) yar kare hakkin mata ce a Kenya, mai fafutukar kare hakkin LGBT kuma mai shirya fina-finai. Ta yi aiki a matsayin mai ba da shawara ga 'yancin al'ummar LGBTQ na Afirka sama da shekaru 20.[1]

Tarihin Rayuwa

gyara sashe

An haifi Kagendo a Kenya kuma tana da ’yan’uwa shida.[2] Ta koma kasar Amurka inda ta shafe tsawon rayuwarta.

Kagendo ta samu digirin ta na BA a fannin nazarin mata daga Jami’ar Rutgers kuma ta ci gaba da karatun MA a fannin yada labarai daga makarantar New School for Social Research. Ta ci gaba da sana’arta na harkar fim a matsayin darakta kuma mai shirya fina-finai. Ta kafa ɗakin shirya fina-finai na Wapinduzi Productions a shekarar 1991 kuma ta yi aiki a matsayin babban mai shirya fina-finai na kusan shekaru 26. Ta ba da labarin fim ɗin 1995 na Amurka These Girls Are Missing.

Ta taka rawar gani wajen samar da matsayin jami'ar shirin Afirka a Hukumar Kare Hakkokin Bil'adama ta 'Yan Luwadi da Madigo ta Duniya. Ta kuma yi aikin sa kai a wajen bikin fina-finan Afirka na tsawon shekaru 15.[3] Ta kuma rike matsayin Program Associate tare da National Black Programming Consortium lokacin da ta kasance mai jagorantar al'umma. A cikin shekara ta 2016, ta yi aiki a matsayin darekta na Kayan Abinci a Cocin St. Mary, Harlem.[3]

A watan Agustan 2021, an sanya ta cikin jerin ta a matsayin ɗaya daga cikin mata bakwai da sukayi fafutuka a Afirka waɗanda suka cancanci labari a Wikipedia ta Global Citizen, ƙungiyar ƙasa da ƙasa da ƙungiyar bayar da shawarwari.[4]

Ta mutu a ranar 27 ga Disamba 2017 tana da shekaru 46 a gidanta a Harlem. An binne ta a gonar danginsu na kasar Kenya.[5]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Kagendo Murungi". AWID. 2018-11-22. Retrieved 2021-08-10.
  2. obituary (2018-01-18). "Kagendo Murungi". Obituary Kenya. Retrieved 2021-08-10.
  3. 3.0 3.1 "Murungi, Kagendo | African Film Festival, Inc". Retrieved 2021-08-10.
  4. "7 Notable African Women Activists Who Deserve Wikipedia Pages". Global Citizen. Retrieved 2021-08-10
  5. "mmoneymaker (2018-01-02). "Remembering Activist Kagendo Murungi". OutRight Action International. Retrieved 2021-08-10.