Kabarin Muhammad Attahiru I, Sarkin Musulmi na 12, wanda ya yi mulki tsakanin watan Oktoban shekarar 1902 zuwa Maris 1903 ya taɓa zama cibiyar yawon buɗe ido. Kabarin dai na nan ne a garin Mbormi mai tazarar kilomita hudu daga garin Bajoga na jihar Gombe a Najeriya.[1]

Shekaru 118 da suka gabata ne Halifancin Sakkwato, Muhammad Attahiru na I ya yi zanga-zanga kan zuwan sojojin Birtaniya a yankin. Ya yanke shawarar barin Sakkwato zuwa Madina, daga karshe ya tsaya a Mbormi domin ya yi amfani da fa'idar katangar tsaronta wajen yakar Sojojin Ingila. Yakin da ya kai ga kawo karshen mulkinsa.[2]

Manazarta

gyara sashe
  1. https://dailytrust.com/tomb-of-sultan-who-fought-the-british-neglected-in-ghostly-mbormi
  2. https://dailytrust.com/despicable-neglect-of-our-history