Justina Agatahi
Ƴar Wasan judoka ce kuma ƴar Najeriya. An haifeta a shekara ta 1989
Justina Agatahi (an haifeta ranar 15 ga watan Agusta, 1989). Ƴar Najeriya ce kuma ƴar wasan judoka ce, wacce ta fafata a rukunin U52kg na mata. Ta lashe lambobin tagulla a Gasar Wasannin Afirka na 2007, Gasar Judo ta Afirka ta 2008 da lambar zinare a Gasar Nabeul ta Duniya, Tunisia.[1]
Justina Agatahi | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Najeriya, 15 ga Augusta, 1989 (35 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | judoka (en) |
Aikin wasanni
gyara sasheA wasannin Afirka na 2007, wanda aka gudanar a Maputo, Mozambique. Ta lashe lambar tagulla a gasar kilo 52.[2]
A gasar Judo ta Afirka ta 2008 da aka yi a Agadir, Morocco, Agatahi ya sake fafatawa a gasar kilo 52 kuma ya lashe lambar tagulla.[3]
Har yanzu a cikin 2008, ta shiga gasar Nabeul ta Duniya, Tunisia kuma ta lashe lambar zinare a cikin gasar U52kg ta mata.[4]
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Justina Agatahi, Judoka, JudoInside". www.judoinside.com. Retrieved 2020-11-20.
- ↑ "African Games Alger, Event, JudoInside". www.judoinside.com. Retrieved 2020-11-20.
- ↑ "African Championships Agadir, Event, JudoInside". www.judoinside.com. Retrieved 2020-11-20.
- ↑ "International Tournament Nabeul Tunisia, Event, JudoInside". www.judoinside.com. Retrieved 2020-11-20.