Julian Nagelsmann
Julian Nagelsmann (an haife shi a ranar 23 ga watan Yuli a shekarar 1987) ƙwararren mai horar da ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Jamus wanda a halin yanzu shine manajan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jamus. Ya taba jan ragamar TSG Hoffenheim da RB Leipzig da Bayern Munich a gasar Bundesliga.
Julian Nagelsmann | |||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Landsberg am Lech (en) , 23 ga Yuli, 1987 (37 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Jamus | ||||||||||||||||||||||||||
Harshen uwa | Jamusanci | ||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Jamusanci | ||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | association football manager (en) da ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga baya | ||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 189 cm |
An haife shi a Bavaria, Nagelsmann ya yi ritaya a matsayin ɗan wasan ƙwallon ƙafa yana da shekaru 20 bayan raunin da ya samu. A shekara ta 2010, ya fara aikin horarwa a matsayin kocin matasa a TSG Hoffenheim, inda daga karshe ya horar da kungiyarsu ta farko a shekarar 2015, inda ya kai su matsayi na uku a gasar Bundesliga da gasar cin kofin zakarun Turai. Ya bar Hoffenheim a cikin 2019 kuma an nada shi a kungiyar ta RB Leipzig ta Bundesliga, inda ya kai wasan kusa da na karshe na gasar zakarun Turai a 2020.
Bayern Munich ta nada Nagelsmann a shekara ta 2021 kan cinikin rikodi a duniya wanda ya kai Yuro miliyan 25 kwatankwacin fam miliyan 21.7, wanda hakan ya sa ya zama koci mafi tsada. Ya lashe kofin Bundesliga a kakar wasa ta farko, amma an kore shi a matsayin koci daga kungiyar a watan Maris 2023.