Jeremiah Dermot O'Connell, MFR (1 ga watan Satumba, alif dari tara da talatin da biyar 1935 zuwa sha hudu 14 ga watan Maris, dubu biyu da goma sha takwas 2018) ya kasance Firist na Katolika, malami, kuma mai gudanarwa, wanda aka san shi a matsayin shugaban makarantar da ya fi dadewa a Najeriya. Ya yi aiki a matsayin shugaban makaranta na tsawon shekaru 50, kuma ya zauna a Najeriya na tsawon shekaru 56.

Rayuwa ta farko da ilimi

gyara sashe

Jeremiah Dermot O'Connell, an haife shi a Cloone, Castletown Roche a County Cork, Ireland. Ya yi karatu a Makarantar Kasa ta Castletown Roche daga alif dari tara da arba'in 1940 zuwa alif dari tara da arba'in da takwas 1948, kafin ya ci gaba zuwa Kwalejin St Colman, Fermoy, inda ya kammala karatun sakandare a matsayin mai shiga. Ya sami takardar shaidarsa a alif dari tara da hamsin da uku 1953 kuma ya shiga Kwalejin Jami'ar Cork, inda ya sami digiri na BA a watan Yunin alif dari tara da hamsin da bakwai 1957. Daga baya, ya ci gaba da karatun tauhidi tare da Ubannin Kiltegan, wanda ya kai ga tsarkake shi a matsayin firist a ranar Lahadi ta Easter, 2 ga Afrilu, alif dari tara da sittin da daya 1961, a Cocin St Mary, Killamoat . [1]

Bayan an naɗa shi a alif dari tara da sittin da daya 1961, O'Connell ya isa kasar Najeriya kuma ya fara aikinsa yana aiki a Cocin Diocese na jihar Calabar a matsayin mai wa'azi na Order of St. Patrick kuma mai kula da Saint na Ireland. Ya yi aiki a makarantar sakandare ta St Columbanus, dake Ikwen a jihar Calabar kafin ya dauki alƙawari a Prefecture na Minna a alif dari tara da sittin da uku 1963. Ya yi aiki a Minna ya kai shekaru hamsin da hudu 54. Da farko yana koyarwa a Kwalejin Horar da Malamai ta St Malachy, ya koma makarantar sakandare ta Fatima (daga baya aka sake masa suna Makarantar Sakandare ta Gwamnati kuma a halin yanzu an san shi da Kwalejin Kimiyya ta Fr O'Connell Minna), inda ya kasance har sai lokacin da ya tashi daga Najeriya a watan Afrilun shekarar dubu biyu da goma sha bakwai wato 2017. Yayinda yake Minna a matsayin shugaban makaranta, ya zauna a cikin majami'u. Shekaru da yawa, ya zauna a cikin majami'ar St Michael's Cathedral Parish sannan daga baya a majami'ar Our Lady of Fatima Parish inda ya kasance Uba-in-Charge wato babban mai gudanarwa.[2]

Don nuna godiya ga hidimarsa, tsohon shugaban kasar Najeriya wato shugaba Olusegun Obasanjo ya girmama shi da girmamawa ta kasa (national honor) na dan kungiya wato memba na Jamhuriyar Tarayya (MFR). An ba shi lambar yabo ta gargajiya ta Jagaban Ilimi Minna (Hasken haske na ilimi a Minna) daga Sarkin Minna, wato Umar Farouq Bahago .

Mutuwa da gado

gyara sashe

Gwamnatin Jihar Nijar ce ta gudanar da bikin tunawa da O'Connell, wacce ta sake canza sunan Makarantar Sakandare ta Gwamnati takoma Fr. Kwalejin O'Connell, Minna, don girmama shi.

Ya mutu a ranar sha hudu 14 ga Maris, 2018.

Bayanan da aka ambata

gyara sashe
  1. "O Fullness". st-patricks (in Turanci). St. Patrick's Missionary Society. Retrieved 3 January 2024.
  2. "Longest Serving Principal In Nigeria, Rev. Fr. O'Connell, Dies". Pearlsnews – Top Entertainment News and Gossip in Nigeria. 20 March 2018. Retrieved 2 January 2024.