Jeanne d'Arc Debonheur lauya ce yar kasar Rwanda hakazalika yar siyasa wadda ta kasance Ministan 'Yan Gudun Hijira da Bala'i na Majalisar Ministocin Rwanda tun daga ranar 30 ga watan Agustan shekarar 2017. [1]

Jeanne d'Arc Debonheur
Rayuwa
Haihuwa Ruwanda, 19 ga Afirilu, 1978 (46 shekaru)
ƙasa Ruwanda
Mazauni Kigali
Karatu
Makaranta National University of Rwanda (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Tarihi da ilimi

gyara sashe

An haife ta ranar 19 ga watan Afrilu 1978, [2] kuma ta halarci makarantun cikin kasar Ruwanda. A shekarar 2012 ta sami digiri na biyu a fannin shari'a daga Jami'ar Kasa ta Rwanda.[2]

Debonheur ta fara aikinta ne a cikin shekarar 2008, tana aiki a matsayin Magatakarda ta Kotu a Kotun Kasuwanci, wanda ke a Musanze da Nyarugenge, tana aiki a wannan matakin har zuwa 2011.

Daga 2011 har zuwa 2012 ta yi aiki a matsayin mai ba da shawara a fannin shari'a kuma mai bayar da shawara a majalisar wakilai ta majalisar dokokin Rwanda. Tsawon watanni uku, daga Janairu 2013 zuwa 23 ga Afrilu, 2013, ta yi aiki a matsayin jami'ar shari'a a "Hukumar Kula da Muhalli ta Rwanda" (REMA). [2] [3]

Daga 24 Afrilu 2013, Debonheur ta yi aiki a matsayin ƙwararrar mai tsara dokoki kuma a matsayin mai bayar da shawara kan shari'a ga Majalisar Dattijan Rwanda, tana aiki a cikin wannan aiki har zuwa 29 Agusta 2017. [2]

A ranar 31 ga Agusta, 2017, an rantsar da ita a matsayin ministar kula da bala'o'i da harkokin 'yan gudun hijira ta kasar Rwanda. [4]

Rayuwa ta sirri

gyara sashe

Jeanne d'Arc Debonheur na da Aure kuma tana da da yara uku. [2]

Manazarta

gyara sashe
  1. KT Press Staff Writer (30 August 2017). "New Prime Minister Announces Cabinet". Kigali Today Press (KT Press). Archived from the original on 5 September 2017. Retrieved 3 September 2017.
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 2.4 Midimar (31 August 2017). "Rwanda Ministry of Disaster Management and Refugees: About the Minister, Jeanne d'Arc Debonheur". Rwanda Ministry of Disaster Management and Refugees (Midimar). Archived from the original on 24 October 2017. Retrieved 24 October 2017. Cite error: Invalid <ref> tag; name "Bio" defined multiple times with different content
  3. REMA (25 January 2013). "REMA staff committed to work hard for a better environment". Rwanda Environment Management Authority (REMA). Archived from the original on 24 October 2017. Retrieved 24 October 2017.
  4. Kimenyi, Felly (31 August 2017). "Rwanda gets new Cabinet, who is in?". Archived from the original on 3 September 2017. Retrieved 24 October 2017.

Hanyoyin hadi na waje

gyara sashe