Janvière Ndirahisha (an haife ta a shekara ta 1966) Malama ce a fannin ilimi kuma 'yar siyasa 'yar ƙasar Burundi. Daga shekarun 2015 zuwa 2020 ta kasance ministar ilimi na Burundi. Ita ce shugabar kungiyar mata ta ƙasa (FNF).

Janvière Ndirahisha
Education minister of Burundi (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa 18 Disamba 1966 (57 shekaru)
ƙasa Burundi
Karatu
Makaranta University of Antwerp (en) Fassara
Jami'ar Burundi
Thesis director Fred Van Oystaeyen (en) Fassara
Sana'a
Sana'a masanin lissafi, ɗan siyasa da Malami

An haifi Janvière Ndirahisha a shekara ta 1966 a Burundi. Ta yi karatu a Jami'ar Burundi kafin ta yi digiri na uku a Jami'ar Antwerp. Fred Van Oystaeyen ne ke kula da rubutunta kan wakilcin Grothiendiek.[1]

An zaɓi Ndirahisha shugabar sabuwar kungiyar mata ta Burundi a shekarar 2013.[2]


A watan Agusta 2015 an sanar da Ndirahisha a matsayin Ministan Ilimi, Ilimi mai zurfi da Bincike na Kimiyya a majalisar ministocin Pierre Nkurunziza.[3] A shekarar 2019 ta koma zama Ministar Ilimi, Fasaha da Koyarwar Sana'a, tare da Gaspard Banyankimbona a matsayin Ministar Ilimi, Ilimi mai zurfi da Bincike na Kimiyya.[4]

A cikin shekarar 2017 Ndirahisha ta sanar da cewa shugabannin makarantun da suka samu nasara a ƙasa da kashi 30% a jarabawar ƙasa za a sallame su, kuma ma’aikatarta ta rufe makarantu da dama da suka faɗi.[5] A shekarar 2018 ma'aikatarta ta haramtawa 'yan mata masu juna biyu zuwa makaranta, matakin da masu fafutukar kare hakkin bil adama a kasar suka yi suka.[6]

Wanda ya gaji Nkurunziza Évariste Ndayishimiye ya cire Ndirahisha daga majalisar ministocin a shekarar 2020.

Manazarta

gyara sashe
  1. Scott W. Williams. "Janviere Ndirahisha". Black Women in Mathematics. Retrieved 21 February 2021.
  2. Diane Uwimana (26 May 2014). "Women's forum: a slow step". IWACU English News. Retrieved 21 February 2021.
  3. "Government of Burundi". Embassy of the Republic of Burundi in Ankara. 24 August 2015. Retrieved 21 February 2021.
  4. "Burundi". The Economist Intelligence Unit. 1 May 2019. Retrieved 21 February 2021.
  5. Diane Uwimana. "Six "unauthorized" basic schools to be closed in Bujumbura". Retrieved 21 February 2021.
  6. Nita Bhalla (4 July 2018). "Burundi school ban on expectant teens 'skewed' against girls' education". Reuters.