Jamila Muhammad Kogi jaruma ce kuma mawakiya a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood tana daya da cikin mawaka mata Dake haskawa a masana antar a yanzun, mawakiya ce Mai Nasibi tana wake Yan siyasa, Yan kwallon kafa da sarakunan, har da wasu manya a kanniwud.[1]

Takaitaccen Tarihin Ta gyara sashe

Cikakken sunan ta shine Jamila muhammad wacce aka Fi sani da suna Jamila kogi. Ana mata lakabi da Kogi ne saboda ita haifaffiyar jihar kogi tayi karatun firamare da sakandiri a jihar neja. Tayi karatun koyon aikin malamta a FCE ZARIA ta Karanci Islamic studies and social studies, tana da burin cigaba da karatu. Tazo jihar kaduna ne domin karatu se Allah yasa ta fada harkan indostiri na kannywood, daga Nan ta nemi zabin Allah SE ya zaba mata Waka, daga jaruma ta koma mawakiya.[2]

Yare gyara sashe

Jamila yaren ibiran koto ne akwai ibiran okene to ita ibiran koto ne.tana Jin yaruka biyar tana jun yaren nufanci, tanajin yaren ibiran na babanta tana Kuma[3] Jin yaren maman ta kakanda , tanajin Hausa tanajin turanci da wasu da dama.

Waka gyara sashe

Ta fara Waka ne saboda tana son fim, da tabi hanyar fim aka kawai mata ka,idojin da baza ta iya bi ba ta koma Waka. Inda ta Sami DJ barde ,ya gwada muryar ta sukai Waka tare. Daga Nan a hankali ta fara har ta gwanance ta shahara.

Waƙoƙin ta.[4]

  • Sarki Ali nuh
  • Ahmad Musa
  • Nijeriya
  • Aure ko karatu

Manazarta gyara sashe

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-31. Retrieved 2023-07-31.
  2. https://m.youtube.com/watch?v=WVurOYo2dnE
  3. https://naijablog.ng/2020/09/19/download-egbura-music-title-eyioyige-by-jameela-kogi-video-audio/
  4. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-31. Retrieved 2023-07-31.