Jamila Abbas
Jamila Abbas (an haife a shekara ta alif dari tara da tamanin da hudu 1984A.c) masaniyar kwamfuyuta ce, injiniyan na'ura mai ƙwaƙwalwa kuma 'yar kasuwa a Kenya.[1] Ita ce ta ƙirƙiro kuma take shugabantar kamfanin MFarm Kenya Limited, wata kungiya ta intanet da ke taimaka wa manoma su sami mafi kyawun kayan gona, iri, samun rahotannin yanayi da kuma bayanan kasuwa.[2] Ta kirkiri M-Farm ne a shekara ta 2010.[1]
Jamila Abbas | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Kenya, 1984 (39/40 shekaru) |
ƙasa | Kenya |
Karatu | |
Makaranta | Strathmore University (en) |
Sana'a | |
Sana'a | computer scientist (en) da ɗan kasuwa |
Kuruciya da Karatu
gyara sasheJamila an haife ta ne a Kenya kuma ta halarci makarantun gwamnati ne a yayin karatun ta na ƙasa da matakin jami'a. Ta halarci Jami'ar Strathmore University, inda ta kammala karatun digiri na farko a fannin Injiniyan na'ura mai ƙwaƙwalwa-(Software Engineering).[3]
Aiki/Sana'a
gyara sasheBayan kammala karatunta daga jami'ar Strathmore, Cibiyar Nazarin Kiwon Lafiya ta Kenya (KEMRI) ta ɗauki hayar Jamila domin aiki. Ta kuma zama memba a iHub, wata ƙungiyar fasaha, inda masu fasaha ke taruwa don musayar ra'ayoyi. A kuma nan ne ta haɗu da Susan Oguya, ƙawarta da suka yi karatun jami'a tare. A watan Satumban shekarata 2010, Jamila da Susan suka yanke shawarar yin wani abu game da halin da kananan manoman kasar Kenya ke ciki, ta hanyar amfani da fasaha.
Matan biyu, sun kuma shiga AkiraChix, wani dandali na mata zalla da ke da sha'awar fasahar sadarwa. A can, suka kuma haɗuwa ƙarin wasu daliban Jami'ar Strathmore guda uku, Linda Omwenga, Lillian Nduati, da Catherine Kiguru. Su biyar ɗin sai suka yanke shawarar shiga IPO48, gasar haɓaka software. Gasar, wanda ya kunshi masu takara kusan mutum 100, an tsara shi cikin ƙungiyoyi goma sha bakwai. Manufar ita ce haɓaka aikace-aikacen kwamfuta, wanda za a iya juyawa zuwa kasuwanci mai gwaɓi, duk a cikin awanni 48.
HumanIPO, daga Estonia ce ta shirya gasar. A watan Nuwamba na shekarar 2011, matan biyar suka lashe gasar, da manhajar su na M-Farm, wanda ya hada manoma da masu samar da kayan gona, da hadin gwiwa da kuma ba su damar samun damar farashin kasuwannin yanzu na kayan da suke samarwa a kan kari. Matan biyar sun sami babbar kyautar KSh1 miliyan (kimanin. US $ 10,000).
Sun yi amfani da kuɗin kyaututtukan nasu wajen kafa kamfanin M-Farm Kenya Limited, tare da Jamila Abbas a matsayin Shugaba, Susan Oguya a matsayin COO . Linda Omwenga da Catherine Kiguru jami'ai ne na talla yayin da Lillian Nduati ita ce jami'ar hulda da jama'a.
Sauran ababen la'akari
gyara sasheAbbas a yanzu haka ita ke rike da mukamin darektan ƙasar na New Vision Foundation, ƙungiya mai zaman kanta ta Minneapolis.
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 AGRA News (24 May 2018). "Jamila Abass: The queen of African Agritech Industry". Westlands, Nairobi: Alliance for a Green Revolution in Africa (AGRA). Archived from the original on 8 May 2019. Retrieved 8 May 2019.
- ↑ NVO (5 February 2017). "Jamila Abbas, tech entrepreneur, to direct New Vision Foundation". New Vision Organization (NVO). Archived from the original on 26 August 2019. Retrieved 20 December 2017.
- ↑ Makeni, John (7 January 2011). "Girls who created social network for farmers". Daily Nation. Nairobi. Retrieved 20 December 2017.