Jamia Binoria Aalamia cibiyar ilimi ce ta Musulunci a Karachi, Sindh kasar Pakistan . An dauke ta daya daga cikin madrassa na zamani.[1][2][3] Noman Naeem shine shugaban (chancellor) na seminary.

Mufti Muhammed Naeem shine wadda ya assa jami’ar jamia Binoria a shekara ta 1978 (Rajab 1398 AH). [4] Yana da alaƙa da Ittehad Tanzeematul Madaris-e-Deeniya (ITMD), ƙungiyar ilimi ta addini guda biyar. A wani lokaci, an ce Jamiah Binoria ta sami mafi girman rajistar ɗaliban ƙasashen waje a kasar Pakistan. Rubuce-rubucen kasa da kasa sun ragu bayan Hare-haren Satumba 11, 2001.[5] A shekara ta alif dubu biyu da biyar 2005, tana da kimanin maza 3,000 da dalibai mata 500, gami da dalibai daga kasar Amurka, da kasar Kanada, da kuma kasar Ingila, da kasar Faransa, da kasar Jamus da Gabashin kasar Asiya.[5]Jamia Binoria kuma tana da darussan ifta ga mata, bayan haka tana kiransu "muftia" (Muftis mata). [6]

A ranar 23 ga watan Yunin shekara ta alif dubu da a shirin 2020, an nada Noman Naeem a matsayin shugaban (ko Shugaban) na makarantar sakandare bayan rasuwar mahaifinsa Mufti Muhammad Naeem ranar 20 ga watan a shekara ta alif dubu biyu da a shirin Yulin 2020.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Renowned religious scholar Mufti Naeem passes away in Karachi". The Express Tribune (in Turanci). 2020-06-20. Retrieved 2021-07-12.
  2. "'Terror' school turns out to be moderate madrassa - CNN.com". edition.cnn.com. Archived from the original on 2021-07-12. Retrieved 2021-07-12.
  3. "Inside a madrassa in Pakistan | Pakistan Today". archive.pakistantoday.com.pk. 13 May 2012. Archived from the original on 2021-07-12. Retrieved 2021-07-12.
  4. "Introduction to Jamia Binoria". Jamia Binoria. Archived from the original on 8 August 2004.
  5. 5.0 5.1 'Madrassas ask for foreign support' BBC News, 2 September 2005
  6. "Remembering Mufti Naeem of Jamia Binoria". July 2020.