Jabir Sani Maihula
Dr Jabir Sani Maihula,(an haifeshi ranar 3 ga watan Yuni, 1981) a garin Sifawa jihar Sakkwato, Najeriya.[1]
Ilimi
gyara sasheYa fara karatun firamare a garin Sokoto, bayan gama karatun firare sai ya garzaya makarantar sakandare ta Kwalejin fasaha ta Rinjin, sokoto. Bayan gama sakandare ya samu gurbin yin karatun digiri a birinin Madina a shekarar 1999, shine ɗalibi mafi ƙanƙantar shekaru a cikin abokan karatun shi. Ya sake cigaba da karatun digiri na biyu a jami'ar East London inda ya karanci Ilimin Addinin Musulunci. A shekarar 2013, ya sake komawa Burtaniya yayi digirin-digirgir a jami'ar Nottingham dake kasar Ingila.
Aiki
gyara sasheJabir ya fara aiki a makarantar koyon shari'a ta sokoto. Bayan dawowarsa Najeriya yayi aiki da jami'ar Usman dan fodiyo.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Ku San Malamanku tare da Sheikh Dr Jabir Sani Maihula". BBC Hausa. 26 February 2021. Retrieved 7 December 2024.