Ismaila Gwarzo
Ismaila Gwarzo tsohon jami’in tsaro da leken asiri ne a Najeriya. Ya kasance dan sanda, kuma darakta na farko a Hukumar Tsaro ta Jiha; Ministan harkokin 'yan sanda kuma ya kasance mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro a lokacin Sani Abacha.
Ismaila Gwarzo | |||
---|---|---|---|
ga Yuni, 1986 - Satumba 1990 | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Gwarzo, | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | civil servant (en) |
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Aliyu Ismaila Gwarzo a ƙauyen Gwarzo da ke jihar Kano, kimanin kilomita 72 daga babban birnin Kano. Ya shiga rundunar 'yan sanda ta Najeriya inda ya rike mukamai da dama na kara daukar nauyi, ya yi ritaya da babban mukami.
A watan Yunin 1986 shugaban mulkin soja Janar Ibrahim Babangida ya nada Gwarzo Darakta Janar na sabuwar hukumar tsaro ta farin kaya (SSS), da ke da alhakin leken asirin cikin gida. Mataimakin Daraktan shine Laftanar Kanal A.K. Togun
Manazarta
gyara sashehttps://www.xyz.ng/en/people/ismaila-gwarzo-biography-fact-career-awards-net-worth-and-life-story-104254[permanent dead link]