Isaac Adebayo Adeyemi Farfesa ne na Najeriya a fannin kimiyyar abinci kuma ɗan ƙwararren Cibiyar Kimiyya ta Najeriya, wanda aka zaɓa a cikin Ƙungiyar Kwalejin a babban taronta na shekara-shekara da aka gudanar a 2012.[1] Shi ne shugaban jami'ar fasaha ta Bells, Jami'a mai zaman kanta da ke Ota, jihar Ogun ta Kudu maso yammacin Najeriya.[2]

Isaac Adebayo Adeyemi
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Ibadan
Sana'a
Kyaututtuka
Mamba Makarantar Kimiyya ta Najeriya

Ya sami digiri na farko a fannin Noma Biochemistry da Nutrition, daga Jami’ar Ibadan a shekarar 1972, sannan ya yi digirin digirgir a fannin kimiyyar abinci daga Jami’ar Leeds da ke United Kingdom a shekarar 1978. Ya fara aiki a shekarar 1973 a Sashin Kimiyar Abincin na Jama’a na Jami’ar Ibadan.[3] Daga baya ya shiga hidimar jami’ar Obafemi Awolowo a matsayin malami na biyu a shekarar 1978 kuma ya kai matsayin Reader a shekarar 1990 a shekarar 1991 aka mayar da shi jami’ar fasaha ta Ladoke Akintola inda aka nada shi Farfesa a fannin ilimin abinci[4]. A watan Agustan 2006, an nada shi shugaban jami'ar fasaha ta Bells, mukamin da ya rike har zuwa yau.[5]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Fellows of the Nigerian Academy of Science". Nigerian Academy of Science. Archived from the original on November 9, 2015. Retrieved September 8, 2015.
  2. "Nigeria loses N75bn to US, European varsities - VCs - Vanguard News". Vanguard News. 6 December 2012. Retrieved 10 September 2015.
  3. "Prof. Adeyemi's Merit Award". Independent Newspapers Limited. Retrieved 10 September 2015.
  4. "PROF. ISAAC ADEBAYO ADEYEMI". nafstsnational.com. Retrieved September 8, 2015.[permanent dead link]
  5. Anozim. "How Buhari can lift education, by academics". The Guardian Nigeria. Retrieved 10 September 2015.