Ireti Heebah Kingibe (an haife ta 2 Yuni 1954) ta kasance injiniyan gine-gine kuma yar siyasa a Najeriya. An zabe ta a majalisar dattawa mai wakiltar Babban Birnin Tarayyar Najeriya (FCT) a zaben Najeriya na 2023 a karkashin Jam’iyyar Labour (LP). Kanwa ce ga Ajoke Mohammed, matar tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya Murtala Mohammed.

Rayuwarta da Ilimi gyara sashe

Kingibe ta fara karatu a makarantar Emotan preparatory, bayan ta halarci makarantar Queen's College Lagos da Washington Irving High School don karatun sakandare. Ta yi digiri a Civil engineering a University of Minnesota.

Ayyuka gyara sashe

Kingibe ta fara aikinta a matsayin Injiniya mai kula da inganci tare da kamfanin Bradley Precast Concrete Inc. daga 1978 zuwa 1979. Daga nan sai ta ci gaba da aiki tare da sashin Ma'aikatar Sufuri ta Minnesota, inda ta kuma yi aiki a matsayin injiniya daga 1979 da 1991. Ta koma Najeriya don shekara guda ta aiki tsakanin 1981 da 1982. An tura ta aiki a matsayin mai kula da aikin tare da sansanin Sojojin Sama na Najeriya a Ikeja, Legas . [1]

Manazarta gyara sashe

  1. "Ireti Kingibe: Biography, Education, Professional and Political Career, Marriage, Net Worth, and Controversy". NewsWireNGR (in Turanci). 2023-02-22. Retrieved 2023-02-28."Ireti Kingibe: Biography, Education, Professional and Political Career, Marriage, Net Worth, and Controversy". NewsWireNGR. 22 February 2023. Retrieved 28 February 2023.