Inumidun Akande[1] An haife ta a ranar 10 ga watan Yuni a shekarar 1947 masaniyar shari'a ce yar Najeriya kuma tsohuwar babban alkalin jihar Legas.[2][3]

Inumidun Akande
Rayuwa
Haihuwa 10 ga Yuni, 1947 (77 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Lagos
Sana'a
Sana'a Lauya

Rayuwar farko

gyara sashe

Ta yi makarantar firamare ta Holy Trinity da ke Ebute Ero, babban birnin jihar Legas kudu maso yammacin Najeriya kafin ta wuce makarantar Grammar ta Ijebu Ode a jihar Ogun a Najeriya, inda ta samu takardar shedar makarantar West Africa a shekarar 1966. Ta samu digirin farko a fannin shari'a.[4] daga Jami'ar Legas a 1970. Ta kammala karatun lauya a Najeriya a 1971 kuma ta samu Call to Bar a ranar 16 ga Yuni, 1971.[5]

Aikin lauya

gyara sashe

Ta shiga aikin shari’a a jihar Legas a farkon shekarun 1970, sannan ta yi aiki a ma’aikatar [6]shari’a a matsayin darakta mai tsara dokoki, kafin ta samu canjin sheka zuwa majalisar dokoki ta kasa, Legas a matsayin mataimakiyar shugabar shari’a a shekarar 1983. An nada ta a benci na Legas. 8 ga Agusta, 1989. An nada ta Babbar Alkalin Jihar Legas a ranar 8 ga Satumba, 2009, shekaru biyu bayan Babatunde Fashola, Gwamnan Jihar Legas ya hau karagar mulki. Inumidun ta yi ritaya daga aiki ne a ranar 10 ga watan Yuni, 2012, tana da shekaru 65 a duniya, inda Ayotunde Phillips ya gaje ta a matsayin babban alkalin jihar Legas na 14.[7][8]

Manazarta

gyara sashe
  1. https://en.wikipedia.org/wiki/Inumidun_Akande
  2. https://archive.today/20150426123618/http://www.thenationonlineng.net/2011/index.php/mobile/society/50216-%E2%80%98she-came,-she-saw,-she-conquered%E2%80%99.html
  3. "Justice Inumidun Akande - P.M. NEWS Nigeria"
  4. https://books.google.com/books?id=sZ1XAAAAQBAJ&q=Inumidun+Akande&pg=PT181
  5. http://www.pmnewsnigeria.com/tag/justice-inumidun-akande/
  6. http://www.channelstv.com/2012/06/09/justice-akande-retires-as-chief-judge-of-lagos-state/
  7. http://saharareporters.com/2013/11/11/seven-nigerian-judges-targets-efcc-corruption-probe
  8. https://archive.today/20150426123613/http://nigeriannotables.com/?p=1111