Introducing the Kujus (fim)
Introducing the Kujus fim din wasan kwaikwayo ne na wasan barkwanci na kasar Najeriya na 2020 wanda Biodun Stephen ya ba da umarni kuma Winifred Okpapi ya shirya shirin. [1] TaurarinFim din ya fito da Bisola Aiyeola, wacce ta shirya fim din. [2] Hakazalika akwai sauran jaruman shirin da suka hada da Timini Egbuson, Femi Jacobs, Bimbo Ademoye, Sophie Alakija da Mimi Onalaja kuma an shirya shirin fim din a Badagry. [3] Fim din ya mayar da hankali ne kan soyayyar wata budurwa ga danginta, da yadda wannan soyayyar ke hada danginta da kawo karshen fadace-fadace. An saki fim din ranar 27 ga watan Nuwamba, shekarar 2020. [4] A makon da aka saki fim din ya samu zunzurutun kudi har miliyan 10. [5] Introducing the Kujus ya dace ga ahali su kalla amma bisa jogarancin iyaye. [6]
Sharhi
gyara sasheIntroducing the Kujus ya ba da labarin wasu ‘yan’uwa ‘yan Najeriya guda biyar da ke tsaka-tsaki. Basu son komawa garinsu Badagry, domin tunawa da rasuwar mahaifiyarsu na tsawon shekaru biyar. Mausi Kuju (da Bisola Aiyeola ya fito a shirin) tare da taimakon Maugbe Kuju ( Timini Egbuson ya fito a matsayin jarumin) suna shirya wani shiri na haɗa sauran ƴan uwansu. Don shirin ya yi nasara, dole ne ta yaudari ’yan’uwanta, amma yanayin dangantakarsu yana nufin ba ta san ainihin yadda abin zai gudana ba.
Yan wasan shirin
gyara sashe- Bisola Aiyeola a matsayin Mausi
- Timini Egbuson a matsayin Maugbe
- Femi Jacobs a matsayin Mautin
- Kunle Remi a matsayin Mauyan
- Ronke Odusanya a matsayin Maupe
- Bimbo Ademoye a matsayin Ebi
- MC Lively a matsayin Barry Wonder
- Sophie Alakija a matsayin Lily
- Folaremi Agunbiade a matsayin Chuks
- Mimi Onalaja a matsayin Pamela
- Chris Iheuwa a matsayin Otunba
- Temitope Ogunleye a matsayin Tombra
- Ayomide Ogunleye a matsayin Bibiana
Kyaututtuka da Ayyanawa
gyara sasheShekara | Kyauta | Iri | Mai karba | Sakamako | Madogara |
---|---|---|---|---|---|
2022 | Africa Magic Viewers' Choice Awards | Best Actor in A Drama | Femi Jacobs | Pending | [7] |
Timini Egbuson | Pending | ||||
Best Art Director | Adeoye Adetunji | Pending | |||
Best Writer | Manie Oiseomaye, Donald Tombia and Biodun Stephen | Pending |
Nassoshi
gyara sashe- ↑ BNTV (November 9, 2020) The Trailer for "Introducing The Kujus" Will Leave You Wanting More Retrieved December 10, 2020
- ↑ Chinonso, Ihekire (September 5, 2020) Bisola gets producer badge in Introducing The Kujus Archived 2024-02-13 at the Wayback Machine Retrieved December 10, 2020.
- ↑ Chinonso, Ihekire (November 7, 2020) Introducing The Kujus beams light on Badagry Archived 2024-02-13 at the Wayback Machine Retrieved December 10, 2020.
- ↑ Precious, Nwogu (November 12, 2020) 'Introducing The Kujus' starring Bisola Aiyeola, Timini Egbuson set for November 27 release Retrieved December 10, 2020.
- ↑ Precious, Nwogu (December 5, 2020) 'Introducing the Kujus' grosses over N10 million in opening week Retrieved December 10, 2020
- ↑ Editor (December 5, 2020) Strong cinema opening weekend for introducing The Kujus Archived 2024-02-13 at the Wayback Machine Retrieved December 16, 2020
- ↑ "2022 Africa Magic Awards Nominees don land- See who dey list". BBC News Pidgin. Retrieved 2022-03-26.