Imelde Sabushimike 'yar siyasar ƙasar Burundi ce wacce ke aiki a matsayin Ministar Kare Haƙƙin Ɗan Adam, Harkokin Jama'a da Jinsi a Burundi, wanda shugaban Burundi, Janar Evariste Ndayyimiyishe ya naɗa. Ita ce macen Twa ta farko da ta shiga cikin Gwamnati a Burundi. [1]

Imelde Sabushimike
Minister of National Solidarity, Social Affairs, Human Rights and Gender (en) Fassara

Rayuwa
ƙasa Burundi
Karatu
Harsuna Faransanci
Kirundi (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imelde Sabushimike

Ilimi da asali

gyara sashe

Sabushimike ta sami digiri a fannin tattalin arziki. Ta yi aiki da Hukumar Tattaunawar Cikin Gida ta Ƙasa a matsayin Sakatariya. [2]

A cikin shekarar 2013, Sabushimike ta yi aiki da wata ƙungiya mai zaman kanta mai suna UNIPROBA (Unissons nous por la promotion des Batwa ko haɗa kai don haɓaka Batwa) wanda aka kafa a cikin shekarar 2003 wanda aka ƙirƙira don kare haƙƙin al'ummar Batwa. Ta yi amfani da wannan kafar wajen taimakawa da inganta rayuwar al’ummar Batwa. An ce Imelde ta yi aiki don tallafawa wani kyakkyawan ci gaba da tsarin zamantakewa, ciki har da ilimi, samar da ayyukan yi, makamashi da sauransu.[1][3]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 Butoyi, Phirmin. "Imelde Sabushimike, First Twa Woman in a Government in Africa : Burundi makes history". AroniSmart (in Turanci). Archived from the original on 2021-06-29. Retrieved 2021-06-29.
  2. "Opposition disappointed by new Cabinet". IWACU English News (in Turanci). Retrieved 2021-06-29.
  3. "Imelde Sabushimike: calling for the protection of Burundi's Batwa community".