Ikuinyi Owaji Ibani ɗan siyasar Najeriya ne kuma kakakin majalisar dokokin jihar Ribas.[1] Daga shekarar 2007 zuwa 2011, ya yi aiki a matsayin memba na Majalisar Dokoki ta Jiha mai wakiltar mazaɓar Andoni, kuma daga shekarar 2011 zuwa 2015, ya kasance Babban Mai Shari'a na Majalisar. Ɗan jam'iyyar PDP ne. A zaɓen Majalisar na 8, ya doke abokin takararsa na jam’iyyar All Progressives Congress da ƙuri’u sama da 50,000.[2]

Ikuinyi O. Ibani
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Sana'a
Imani
Jam'iyar siyasa Rivers State People's Democratic Party (en) Fassara

A ranar 19 ga watan Disamban 2015, Ibani ya sanar da murabus ɗinsa daga ofishin shugaban majalisar, bisa dalilai na kansa. An maye gurbinsa da Adams Dabotorudima daga Okrika.[3] A cikin watan Disamban 2016 ne aka sake zaɓen Ibani a matsayin shugaban majalisar dokokin jihar Ribas.[4]

Duba kuma gyara sashe

  • Jerin mutanen jihar Ribas

Manazarta gyara sashe