Ifeoluwa Ehindero ɗan siyasan Najeriya ne kuma mai tallafawa al'umma. Shi ne ɗan majalisar wakilai mai wakiltan Akoko North East/Akoko North West bayan lashe zaɓen fidda gwani na tikitin jam'iyyar All Progressives Congress. [1] [2]

Ifeoluwa Ehindero
Rayuwa
Haihuwa 17 Satumba 1985 (39 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

A matsayinsa na mai ba da taimako, ya ba da gudummawa ga fannin kiwon lafiya, ilimi da noma a al'ummarsa. [3] [4]

Aikin siyasa

gyara sashe

Ehindero ya tsaya takarar ne a matsayin mamba mai wakiltar Akoko North East/Akoko North West a majalisar wakilai wanda ya maye gurbin Tunji Bunmi Ojo bayan naɗa shi ministan harkokin cikin gida da shugaba Bola Tinubu yayi. [5] Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta gudanar da zaɓen na bankwana a ranar 3 ga watan Fabrairun 2024, wanda ya lashe da kuri’u 35,504 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Olalekan Bada daga jam’iyyar Peoples Democratic Party wanda ya samu kuri’u 15,328. [6]

Manazarta

gyara sashe
  1. David (17 October 2023). "Ehindero signifies intention to contest Akoko East/North federal constituency poll". The Sun Nigeria (in Turanci). Retrieved 16 October 2024.
  2. "APC's Ehindero Wins By-election in Ondo". www.thisdaylive.com. Retrieved 16 October 2024.
  3. "Ondo Rep, Ife Ehindero Awards Scholarship to UTME Top Performer | TheCity". THE CITY (in Turanci). 8 May 2024. Retrieved 16 October 2024.
  4. tvcnewsng (22 September 2024). "Lawmaker, Ehindero distributes bags of fertilizers to farmers in Akoko federal Constituency – Trending News" (in Turanci). Retrieved 16 October 2024.
  5. David (17 October 2023). "Ehindero signifies intention to contest Akoko East/North federal constituency poll". The Sun Nigeria (in Turanci). Retrieved 16 October 2024.
  6. Dada, Peter (6 January 2024). "Ondo youths back Ehindero's son ahead of bye-election". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 16 October 2024.