Idris Garba Kareka ɗan siyasan Najeriya ne haifaffen Jahun jihar Jigawa. Yana wakiltar mazaɓar Jahun a majalisar dokokin jihar Jigawa a ƙarƙashin jam’iyyar APC, kuma ya zama kakakin majalisar jihar Jigawa ta bakwai.[1]

Idris Garba Kareka
Rayuwa
Sana'a

Tsigewa gyara sashe

Jim kadan bayan kammala zaɓen shekarar 2015 da kuma majalisar dokokin jihar Jigawa ta 6 a watan Yuni, ƴan majalisar sun zaɓi Garba a matsayin kakakin majalisar.[2] A ranar 3 ga watan Janairun 2017 ƙasa da watanni bakwai da rantsar da shi, mambobin 25 daga cikin 30 sun yi kira da a tsige shi ba tare da wata tangarda ba a lokacin da gwamnan ya tafi kasar waje. Dalilan da suka sa aka tsige shi dai Garba ya ki amincewa da bukatar abokan aikinsa, kuma ya yi ikirarin cewa ya yi wa kansa ƙarfin tuwo, wanda hakan ya sa abokan nasa suka daina amincewa da shi.[3] Jim kadan bayan zaɓen 2019, an ƙaddamar da majalisar jihar Jigawa ta 7 a watan Mayu kuma aka sake zaɓen Garba a matsayin kakakin majalisar.[4][1]

Nassoshi gyara sashe

  1. 1.0 1.1 "JUST IN: Jigawa Assembly re-elects impeached Speaker". The Nation. 13 June 2019.
  2. "Jigawa Assembly Speaker emerges". The Nation. Lagos, Nigeria. 11 June 2015. Retrieved 17 June 2021.
  3. "Real Reasons Why Former Jigawa Speaker, Idris Garba Was Impeached". Universal Reporters. 5 January 2017. Retrieved 17 June 2021.
  4. Lenbang, Jerry (9 May 2019). "Jigawa house of assembly removes speaker". The Cable. Lagos, Nigeria.