Ibrahim Khalid Mustapha

Ɗan Siyasar Najeriya

Ibrahim Khalid Mustapha ɗan siyasar Najeriya ne kuma ɗan majalisar dattawa mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya ta 10. Ya doke abokin hamayyarsa Sulaiman Abdu Kwari, bayan an zaɓe shi a babban zaɓen Najeriya na shekarar 2023, ɗan jam'iyyar PDP ne.[1][2][3]

Ibrahim Khalid Mustapha
Rayuwa
Sana'a

Zaɓen Fidda Gwani

gyara sashe

Mustapha ya lashe zaɓen fidda gwani na jam'iyyar PDP da ƙuri'u 257, wanda hakan ya bashi damar zama ɗan takarar jam'iyyar PDP a hukumance a babban zaɓen Najeriya na shekarar 2023 da ta gabata.[4] Bayan fafatawa da sukayi da abokin takararsa Sulaiman Abdu Kwari, a ƙarshe kuma yayi Nasara ya lashe zaɓen.

Manazarta

gyara sashe
  1. Sahabi, Ahmad (28 February 2023). "#NigeriaDecides2023: PDP wins ALL Kaduna senatorial seats". The Cable. Retrieved 7 December 2023.
  2. "PDP wins Kaduna North Senatorial Seat" (in Turanci). Premiumstimesng.com. 27 February 2023. Retrieved 7 December 2023.
  3. Enyiocha, Chimezie (28 February 2023). "2023 Elections: PDP Clears All Three Kaduna Senatorial Seats". channelstv. Retrieved 7 December 2023.
  4. "Mustapha wins PDP ticket for Kaduna North Senatorial District". premiums times. 24 May 2022. Retrieved 7 December 2023.