Malam Ibrahim Adam Usman wanda aka fi sani da Al-Madani ya kasance ɗaya ne daga cikin fitattun malamai dake a ƙasar Najeriya, (An haife shi a ranar 24 ga watan Yuni 1977) a Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya. Malam Ibrahim Adam ya fi bayar da fatawa akan lamuran da suka shafi aure da kuma zamantakewar auren, saboda an fi yi masa tambaya a kan lamuran.[1]

Tarihin Rayuwa

gyara sashe

Malam Ibrahim Adam an haife shi a Jihar Kaduna a Najeriya[2], mahaifinsa ba malami ba ne ɗan kasuwa ne, amma Allah ya sa yana da sha'awar karatu, wanda hakan ya sanya tun da suka tashi suke fagen neman ilimi. Mahaifinsa ya sanya shi makarantar Islamiyya, amma tasirin abokai ya sanya yake bin abokansa zuwa makarantarsu ta allo. Ya yi ɓangaren karatun boko amma ya tsaya ne a iya matakin sakandire, sai dai a ɓangaren karatun Addini ya tiƙe har digiri na biyu, wanda kuma a yanzu haka yana kan yin na ukku. Malam ya samu damar haddar Al-Qur'ani mai girma kuma ya fi son karanta Suratu Nahli.

Malamansa

gyara sashe

Malam Ibrahim yayi karatu a gaban malamai da yawa ciki da wajen Najeriya, yace wasu ma bazai iya tuna su ba. Cikin Malaman da ya tasirantu da su akwai:

A Madina ya yi karatu a wajen,

  • Farfesa Sulaiman Ruhaili wanda a hannunsa ya yi karatun Tauhidi, Sheikh Abdul-Muhsunil Abbad, Sheikh Abdul'Aziz Ɗuwaiyyan.

Allah ya saka musu da Alkhairinsa.

Malam Ibrahim yana da mata uku da 'ya'ya takwas.

Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.bbc.com/hausa/articles/crgzzjwnejno.amp
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2024-09-03. Retrieved 2024-09-03.