Hurricane Barbarossa
Yunkurin dakatar da harkar mai a Jihar Ribas.
Shirin Hurricane Barbarossa dai, wani jerin hare-hare ne da ‘yan bindiga suka kai a Najeriya da nufin durƙusar da harkar mai a jihar Rivers.[1] Tun a ranar 14 ga watan Satumban 2008 ne ƙungiyar MEND mai fafutukar ‘yantar da yankin Neja Delta ( MEND ) ta ƙaddamar da ita, amma bayan mako guda ƙungiyar ta sanar da tsagaita bude wuta, bayan ta sha asara mai yawa a hannun sojojin Najeriya.
Iri | rikici |
---|---|
Bangare na | Rikici a yankin Neja Delta |
Kwanan watan | 27 Satumba 2008 |
Wuri | Jihar rivers |