Hukumar Birnin Kaduna
Hukumar Babban Birnin Kaduna na daya daga cikin, manyan hukumomin Kaduna guda uku a jihar Kaduna,[1] Najeriya. Hukumar tana kula da kananan hukumomi 4 cikin 23 a jihar Kaduna, wato; Kaduna North, Kaduna South, Chikun and Igabi local governments. A shekarar 2021 ne aka kafa dokar da ta kafa hukumar babban birnin Kaduna. A da ana kiran hukumar da babban birnin Kaduna ne karamar hukumar Kaduna [2] bayan da aka mayar da birnin Kaduna a matsayin babban birnin jihar a shekarar 1937. Karamar hukumar wata halitta ce ta mulkin mallaka na Burtaniya don kula da haraji, samar da kayan amfanin gona da fitarwa zuwa Burtaniya. [3] Hakimin gundumar, Aminu Sambo ne ya fara jagorantar hukumar a shekarar 1937. Samuel Aruwan mai kula da babban birnin Kaduna a halin yanzu.
Hukumar Birnin Kaduna |
---|
Masu gudanarwa | Shekaru a hidima |
---|---|
RG Adams | 1956-1960 |
Umar Audi | 1960-1961 |
Abubakar Kigo | 1961-1963 |
Abubakar Umar | 1963-1965 |
Abubakar Garba JA AbdulKadir | 1965-1966 |
Abba Dabo Sambo | 1966-1968 |
Sa'idu Barda | 1968-1969 |
Shehu Sulaiman | 1969-1970 |
Magaji Muhammad | 1970-1975 |
Balarabe Mahmud | 1975-1976 |
Ahmad Bakori | 1976-1979 |
Muhammad Hafiz Bayero | 2021-2023 |
Samuel Aruwan | 2023 - kwanan wata |