Hukumar Ƙididdiga ta Jihar Legas
Hukumar Ƙididdiga ta Jihar Legas |
---|
Hukumar kididdiga ta Legas wani sashe ne a ma’aikatar tsare-tsare da kasafin kudi ta jihar Legas da ke da alhakin tsara ayyukan kididdiga a jihar Legas, jiha mai dauke mafi yawan al’umma a Najeriya.[1] Sashen yana mai da hankali kan tarin bayanan ƙididdiga akan batutuwan da suka haɗa da yawan jama'a, gidaje, kuɗi, ilimi, kiwon lafiya, aikin gona, da ayyukan jin daɗin jama'a. Sashen yana kuma haɗin gwiwa da hukumomin ƙasa da ƙasa, gwamnatocin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi, da sauran hukumomin ƙididdiga.[2]
Wallafe-wallafe
gyara sasheƘididdiga na ɗaya daga cikin wallafa na shekara-shekara na sashen. Ya ƙunshi bayana ƙididdiga akan harkokin zamantakewar tattalin arziki na Jiha.[3] Yana fitar da bayanai kan yawan jama'ar Jiha, Gudanar da zirga-zirga, Gudanar da sharar gida da muhalli. Hakanan yana ba da bayanai game da rajistar Motoci, Hatsarin Hanyoyi, Gudanar da zirga-zirga, Gidajen Farashi, da dai sauransu.[4] Sauran wallafe-wallafensu sun haɗa da Ƙididdiga na yawan mutanen Kananan Hukumomi, Basic Statistical Hotline, Wallafi na Ƙididdigan Farashi, Littafin Ƙididdiga na Shekara da kuma Ƙididdigan Motoci da ababen hawa.[5]
Shiri
gyara sasheDon ci gaba da zama wurin tsayawa ɗaya na jihar don ƙididdiga masu inganci, abin dogaro, kuma tsayayyu.
Manufa
gyara sasheTabbatar da tsarin ƙididdiga na dijital, ingantacce, kuma akan lokaci don tsarawa, tsara manufofi, da yanke shawarwari.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "LASG, Ikorodu residents discuss urban renewal". The Punch. Archived from the original on 26 June 2015. Retrieved 26 June 2015.
- ↑ "Residents lament pains of fuel scarcity". The Punch. Archived from the original on 26 June 2015. Retrieved 26 June 2015.
- ↑ "Lagos seeks hitch-free implementation of Ikorodu masterplan". The Guardian Nigeria. Retrieved 26 June 2015.
- ↑ Lagos state health management agency bill has been signed into law". businessdayonline.com. Retrieved 26 June 2015.
- ↑ "Lagos begins re-validation of cooperative societies". The Punch - Nigeria's Most Widely Read Newspaper. Archived from the original on 26 June 2015. Retrieved 26 June 2015.