Abdullahi Iliyasu Yaryasa ɗan siyasar Najeriya ne.

Rayuwar Farko da Karatu gyara sashe

 

An haifi Abdullahi Iliyasu Yaryasa a garin Yaryasa Cikin Gari na karamar hukumar Tudun Wada a ranar 6 ga Fabrairu, 1968.

Daga 1975 zuwa 1981 ya halarci Makarantar Firamare ta Yaryasa.

 

Daga nan ya wuce Sakandire ta Kwalejin Gwamnati a Tudunwada. ↵Abdullahi ya halarci Kwalejin Fasaha ta Gwamnati (GTC), Bagauda don karatun sakandare a tsakanin 1986 zuwa 1989. [1]

Tsakanin 1997 zuwa 2000, Honorabul Abdullahi ya halarci Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Kano inda ya samu takardar shaidar Digiri. Ya samu babbar difloma ta kasa (HND) daga Nuhu Bamalli Polytechnic, Zaria tsakanin 2014 - 2016. [2]

Sina'a da Siyasa= gyara sashe

Ya kasance Wanzami sannan kuma manomi kuma dan siyasa.

Siyasa gyara sashe

Honorabul Abdullahi an fara zaben shi a matsayin Kansila na gundumar Yaryasa tsakanin shekarar 1990 - 1993. A shekarar 2003 aka nada shi mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa ga Shugaban zartarwa na karamar hukumar Tudun Wada kafin a zabe shi. Dan majalisar dokokin jihar Kano a shekara ta 2007-2011, 2011-2015, 2015-2019 Ya yi aiki na tsawon shekaru goma sha biyu (12) sannan aka sake zabar shi a shekarar 2019. A halin yanzu yana kan wa’adinsa na hudu a matsayin dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Tudunwada. Kuma shine yake rike da mukamin deputy majority leader na zauren majalisar jihar kano.

Manazarta gyara sashe