Hon. Hamza Zubairu Masu (An haifeshi ne a ranar 3 ga watan Satumba a shekara ta alif dari tara da sittin da takwas 1968) a kauyen Masu da ke karamar hukumar Sumaila, Jihar Kano.

Ya yi makarantar firamare ta Masu daga shekara ta alif dari tara da saba'in da shida 1976 zuwa alif dari tara da tamanin da biyu 1982. Ya yi Karamar Sakandare a Wudil Teachers College a shekara ta alif dari tara da tamanin da biyu (1982 zuwa 1985). yayi babbar makarantar Sakandare ta kimiyya dake Dawakin Kudu a shekara ta alif dari tara da tamanin da biyar (1985 zuwa alif dari tara da tamanin da takwas 1988). [1]

Bayan nan ya samu gurbin shiga Kwalejin horas da Malamai ta Gumel don samun shaidar shaidar karatu ta kasa (NCE) a fannin Physics/Chemistry a shekara ta (1988 zuwa 1991). Neman ilimi ya kai shi Jami’ar Bayero Kano inda ya sami digiri (B.Sc. Ed) a fannin Geography. Honourable Masu kuma yana da takardar shaidar kammala digiri (PGD) a fannin Gudanarwa. [2]

Daga shekara ta alif dari tara da casa'in da shida 1996 zuwa alif dari tara da casa'in da tara 1999 ya zama zababben kansila sannan a shekara ta 2001 aka nada shi kansila mai kulawa. Honorabul Masu ya zama shugaban karamar hukumarsa wa’adi biyu 2 a shekarar: 2004 zuwa shekara ta 2007 da 2011 kuma da 2015 bi da bi). A shekara ta 2007 ya yi aiki a matsayin mataimakin jami'in gudanarwa na wucin gadi. [3] Tun da farko ya kasance mataimakin jami'in ilimi na (AEO) a ma'aikatar ilimi ta jiha inda ya yi aiki a matsayin malamin makaranta.

kuma yanzu Shine Deputy Speaker zauren majalisar jaha ta kano.

Manazarta

gyara sashe