Hauwa Shariff (Mimi) jaruma ce a fim Mai dogon zango na Tashar Arewa 24 ke shiryawa Mai suna KWANA CASA,IN, sannan ma,aikaciya a Tashar Arewa 24, Kuma fitacciyar mawakiya inda ta fara wakarta Mai suna " malamai Kuna da mahimmanci".[1]

Takaitaccen Tarihin Ta gyara sashe

Cikakken sunan ta shine Hauwa muhammad Shariff wacce akafi sani da mimin Waka, ta fara Waka ne tun tana islamiyya tun ana rera mata har ta fara, tazo tana kallon fina finan hausa daga taji tana son ta Bada nata gudummawar a harkan. Ita tayi wakar "halin Maza" sannan tana kwaikwayon wasu mawakan a muryarsu kamar fati nijar da Kuma mawaki naziru m Ahmad[2]

Manazarta gyara sashe

  1. https://www.dandalinvoa.com/amp/3833179.html
  2. https://m.youtube.com/watch?v=EvawLMEVTZ8